A ranar 4 ga watan Disamba, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya gabatar da jawabi a taron dandalin hadin gwiwar kasuwanci tsakanin Sin da Amurka, wanda Majalisar habaka cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin (CCPIT) da Cibiyar Meridian ta kasa da kasa suka dauki nauyin shiryawa.
Jakada Xie ya ba da shawarar cewa, ya dace ‘yan kasuwa na kasashen biyu su mai da hankali kan jerin abubuwa uku don kara samun kuzari. Na farko, a ci gaba da fadada jerin abubuwan tattaunawa. Sannan akwai bukatar ‘yan kasuwa su tallafa wa gwamnatocin kasashen biyu da dukkan sassan al’umma wajen yin mu’amala da juna a-kai-a-kai, da kuma amfani da tsarin tuntuba kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.
Na biyu, a ci gaba da tsawaita jerin hadin gwiwa, ta yadda kasuwancin Sin da Amurka za su iya amfani da damar hadin gwiwa a sabbin fannoni da masana’antu da kuma samar da karin hadin gwiwa da za a aiwatar a aikace. A lokaci guda kuma, ana sa ran gwamnatin Amurka ta samar da yanayi na gaskiya da adalci, wanda ba ya nuna wariya ga kasuwancin Sinawa na zuba jari da kuma gudanar da harkokinsu a nan.
Na uku, ya kamata a ci gaba da rage jerin matsalolin da ke kasa. Ana fatan shugabannin ‘yan kasuwan Amurka za su taka rawar gani ta hanyar yin kira ga tsirarun ‘yan siyasar Amurka da su dakatar da bata wa kasar Sin suna, da kuma samar da kuzari mai alfanu, maimakon kawo sabbin cikas, domin kyautata dangantakar tattalin arziki da cinikayyar bangarorin biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














