Wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta roki kotun shari’a musulunci da ke zamanta a Magajin Gari a Jihar Kaduna, da ta raba aurenta da mijinta, Alhaji Ali Garba, bisa yawan bukatar jima’i da yake yi.
Mai shigar da karar ta shaida wa kotu a ranar Laraba cewa Garba, ya kan bukaci yin jima’i da ita ko da tana jinin haila da kuma lokacin azumin Ramadan.
- Matsalar Karancin Iskar Gas Na Addabar Turai Yayin Da Amurka Ke Kulla Makarkashiya
- IMMOWA Ta Horar Da Mata Da Yaran Jami’an Shige Da Fice Sana’o’i
Ta ce sun shafe shekara guda a matsayin ma’aurata, inda ta kara da cewa ta koma gidan iyayenta saboda girman abun.
Mai shigar da karar ta bayyana cewa, a zaman da suke tare, Garba yakan dawo gida da rana lokacin da take jinin al’ada domin saduwa da ita, wanda hakan ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.
“Lokacin azumin Ramadan, yakan dawo gida da rana ya nemi yin jima’i, duk lokacin da na ki, sai ya yi fushi.
“Kuma idan na tambaye shi abinci, yawanci ya kan amsa cewa in je in hadu da saurayina ya ciyar da ni.
“Bai taba yarda da ni ba har bai taba barin wani daga ‘yan uwana maza ko mata su ziyarce ni ba,” kamar yadda ta shaida wa kotu.
Matar ta ce ta gudu daga gidan aurenta, saboda ba za ta iya gamsar da mijinta ba sakamakon tsananin sha’awa da yake da shi.
Don haka, ta roki kotu da ta raba auren, domin ba ta shirya saba wa Allah ba akan mijinta ba.
Sai dai mijin ya musanta zargin karar da matar tasa ta shigar a gaban kotu.
Garba, ya shaida wa kotun ta bakin lauyansa, Mista M.A Sambo, cewa mahaifiyar matarsa ta je gidansa ba ya nan, ta kwashe kaya tare da sayar da kadarorinsa, kafin ta tafi da diyarta.
Ya ce mahaifiyar ta yi alkawarin mayar da duk abin da suka kwaso daga gidansa a wani zaman sulhu da aka yi.
Ya lissafa abubawan da aka kwashe masa da suka hada da kujeru na Naira 100,000, talabijin, firij guda biyu, faranti na Naira 35,000 da sauran kayayyakin kicin, kafet da katifa ta Naira 15,000.
Garba ya roki kotu da ta duba bukatarsa ta a mayar masa da kadarorinsa a matsayin sharadin amincewa da bukatar sakin matar tasa.
Alkalin kotun, Murtala Nasir, bayan ya saurari dukkan bangarorin biyu, ya umarci mai kara da ta zo kotu tare da mahaifiyarta a zaman a gaba.
Ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraren karar.