Alkaluman kididdiga da mahukuntan kasar Sin suka fitar a jiya Litinin, sun nuna yadda jimillar cinikayyar hajojin shige da fice na kasar ta karu da kaso 3.6 bisa dari cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, daidai da karuwar kudin kasar har yuan tiriliyan 41.21, wato kusan dalar Amurka tiriliyan 5.82.
Kazalika a watan Nuwamba kadai, alkaluman adadin hajojin shige da fice na Sin sun daga da kaso 4.1 bisa dari a mizanin shekara zuwa kudin kasar yuan tiriliyan 3.9.
Tun daga farkon bana, sakamakon yanayin kasa da kasa mai sarkakiya da sauye-sauye, ya sa kasar Sin ta aiwatar da manufofi masu nagarta bisa manyan tsare-tsare, ta yadda tattalin arzikin kasar ya gudana bisa daidaito ba tare da tangarda ba.
Kafofin yada labaru na kasa da kasa sun yaba da yadda tattalin arzikin kasar Sin ya gudana ba tare da matsala ba, duk da yanayin duniya mai sarkakiya da sauye-sauye. Yadda cinikayyar waje ta Sin ta karu cikin watanni 11 na bana, ya nuna kwazon kasar Sin na raya tattalin arzikinta bisa daidaito da juriya, inda kuma kasar ta samu ci gaba.
Ana dab da kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 cikin nasara. Haka kuma za a fara shirin na 15. A jiya Litinin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS ta shirya wani taro, inda aka yi nazari kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2026, a kokarin kaddamar da shirin na 15 ba tare da matsala ba. A yau Talata kuma, kasar Sin za ta tattauna da wasu hukumomin kasa da kasa guda 10 masu nasaba da tattalin arziki, dangane da shugabancin duniya, da raya duniya tare.
Kasashen duniya na jiran damammakin da kasar Sin za ta samar musu, da kuma fatan yin hadin gwiwa da Sin domin samun nasara tare. Kamar yadda babban sakataren kungiyar kasuwanci ta Masar da Sin Diaa Helmy ya bayyana, yana mai cewa yadda kasar Sin take kiyaye bude kofa ga kasashen waje, ya samar da karin babban kuzari ga wadatar duniya. (Tasallah Yuan)














