Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin Kamfanonin Dangote, ya bayyana damuwa kan abin da ya kira makirci da bita da ƙulli a ɓangaren tacewa da rarraba man fetur a Nijeriya, yana cewa ƙarfin ƙungiyoyin da ke da hannu ya fi na manyan ƙungiyoyin fataucin miyagun kwayoyi.
Da yake jawabi ga manema labarai a Lekki, Dangote ya ce matatar Dangote da kuma matatun mai na gwamnati sun fuskanci hare-haren lalatawa da satar kayayyaki akai-akai, ciki har da cire muhimman sassan injina domin durƙusar da aiyukansu. Ya bayyana cewa ana lalata bututun mai a faɗin ƙasar baki ɗaya, lamarin da ba za a iya danganta shi da cewa haɗari ko yanayi ne sanadi ba.
- Kamfanin Dangote Ya Shiga Sahun Manyan Masu Ɗaukar Nauyin Bikin Bajekoli A Kano Na 2025
- Trump Na Murna Sosai Da Samar Da Matatar Manmu – Dangote
Dangote ya ce Nijeriya ta taɓa dogaro da bututun mai wajen jigilar kayayyaki zuwa rumbunan ajiya 22, amma yanzu duk sun lalace. Ya bayyana asarar da matatarsa ta yi da ta kai kusan dala miliyan 82 sakamakon sata da lalatawa, lamarin da ya tilasta musu ɗaukar matakan tsaro masu tsauri.
Ya jaddada cewa irin wannan lalatawa, na barazana ga samar da mai da tattalin arziƙin ƙasa gaba ɗaya, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙungiyoyin da ke cin gajiyar durƙusar tsarin makamashi a Nijeriya.














