A yau Talata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta fitar da shawarar daukar matakan kakkaba takunkumi kan tsohon shugaban rukunin tsaron kasar Japan Iwasaki Shigeru.
Ma’aikatar ta ce ta bayyana a fili cewa, Iwasaki Shigeru yana hulda da kungiyoyin ‘yan aware na “Taiwan”, wanda hakan ya sabawa ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya”, da kuma ruhin takardu hudu na siyasa tsakanin Sin da Japan, kana hakan tsoma baki ne cikin harkokin cikin gida na Sin, matakin da ya illata ikon mulkin yankin Sin. Bisa dokar “Mayar da martani ta takunkumi daga kasashen waje ta Jamhuriyar Jama’ar Sin”, Sin ta yanke shawarar daukar matakan kakkaba takunkumi kan Iwasaki Shigeru.
Na daya, za a daskarar da kadarorinsa dake cikin kasar Sin. Na biyu kuma, Sin za ta hana kungiyoyi, da daidaikun mutane na cikin kasar Sin yin cinikayya, da hadin gwiwa, da sauran ayyuka tare da shi. Na uku, za a dakatar da ba shi biza, da hana shi shiga kasar Sin, ciki har da yankunan Hong Kong da Macao.
Wannan mataki ya fara aiki tun daga yau Litinin 15 ga watan nan na Disamban 2025. (Amina Xu)














