A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da kantoman yankin musamman na Hong Kong John Lee, wanda ke ziyarar aiki a birnin Beijing.
Yayin tattaunawarsu, Xi ya saurari rahoto dangane da halin da yankin Hong Kong ke ciki, da aikin gwamnatin yankin na Hong Kong daga John Lee.
Shugaba Xi ya ce gwamnatin tsakiya ta gamsu matuka da aikin Lee da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong. Ya kuma yi kira ga gwamnatin yankin musamman na Hong Kong da ta yi aiki tukuru wajen daidaita tafiya da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, da goyon baya da inganta jagorancin gwamnati, da ingiza bunkasar tattalin arziki bisa babban matsayi, da shiga a dama da yankin a fannin bunkasa yankin Greater Bay na Guangdong da Hong Kong da Macao, ta yadda Hong Kong zai dunkule da kasancewa ginshikin ci gaban kasa a dukkanin fannoni bisa managarcin tsari. (Saminu Alhassan)














