Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wata mota da ta yi jigilar giya daga Jihar Legas zuwa Kano.
Mataimakin Kwamandan Hukumar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya tabbatar wa manema labarai da faruwar lamarin, yana mai cewa, “an gudanar da samamen ne bayan mun sami sahihan bayanai kan jigilar kayan giyan.”
- Da Ɗumi ɗumi: Mafarkin Nijeriya Na Zuwa Gasar Kofin Duniya Na Dab Da Cika
- Buhari Ya Dakatar Da Cire Tallafin Man Fetur Ne Saboda Tsoron Juyin Mulki
Ya bayyana cewa, jami’an da ke aiki a Sashen Fagge, sun yi aiki cikin gaggawa bayan samun bayanan sirrin, inda suka yi nasarar tsayar da motar, sannan suka ƙwato giyar.
A cewar Dr. Mujahideen, binciken farko ya nuna cewa wata mata ce ta aiko da giyar zuwa Kano. Ya kara da cewa an kama katon 13 na giya iri-iri daban-daban a lokacin binciken.
An kama direban motar wanda a halin yanzu yake amsa tambayoyi.
Dr. Mujahideen ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa kokarin Hisbah ta hanyar bayar da rahoton ayyukan da suka saba wa dokokin Musulunci a Jihar.














