Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa ta karɓi ƙorafi a rubuce daga attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote kan Shugaban Hukumar NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed.
Dangote ya zargi Ahmed da kashe kusan dala miliyan biyar, wanda ya kai kimanin Naira biliyan bakwai, wajen biyan kuɗin makarantar ’ya’yansa huɗu a ƙasar Switzerland.
- Wakilin Sin Ya Sake Gargadin Japan Da Ta Janye Kalamanta Na Kuskure
- Tsohon Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, Ya Rasu
Haka kuma ya zarge shi da yin ayyukan da ke raunana matatun mai na cikin gida tare da fifita masu shigo da man fetur daga waje.
Mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya ce ɗaya daga cikin lauyoyin Dangote ne, ya miƙa ƙorafin a ranar Talata.
Ya ƙara da cewa a baya hukumar ba ta karɓi irin wannan ƙorafi ba, saɓanin wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai.
Odey, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa ICPC za ta yi cikakken bincike kan dukkanin zarge-zargen da ke cikin ƙorafin.
Ya ce hukumar za ta gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci.
Ya ƙara da cewa ICPC za ta ɗauki matakan da suka dace bisa sakamakon binciken da za a yi, kamar yadda doka ta tanada.














