Ministan harkokin sadarwa, da fadakarwa, da hidimomin rediyo na kasar Zimbabwe, Jenfan Muswere, ya bayyana cewa, majalisar ministocin kasar ta amince da kafa huldar hadin gwiwa tare da wani kamfanin kasar Sin, don kafa wani kamfanin samar da makunnan wutar lantarki na zamani, da kuma na cajin motoci masu amfani da wutar lantarki.
Minista Muswere, ya ce bisa la’akari da yanayin habakar tsarin samar da wutar lantarki a kasar Zimbabwe, kasar tana bukatar karin na’urorin makunnin lantarki, kana ana kara watsi da na’urorin da ba na zamani ba. Ya ce, kafa huldar hadin gwiwar zai samar da dama ga kasar Zimbabwe, ta zama kasa mai samar da na’urorin makunnin lantarki a shiyyarta.
Kazalika, jami’in ya kara da cewa, yin amfani da wani nau’in na’urar zamani dake aiki a matsayin mitar awon wutar lantarki, zai taimaki kamfanonin samar da hidimomi ga al’umma na kasar, ta yadda za su iya kidaye yawan wutar lantarki yadda ya kamata, da kuma samar da damar cajin motoci masu amfani da wutar lantarki, a kokarin dacewa da yanayin duniya a fannin zirga-zirga. (Zainab Zhang)














