A yau Alhamis 18 ga wata ne memban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta ta wayar tarho, da mataimakin firaminista, kuma ministan wajen kasar Cambodia Prak Sokhonn, da ministan wajen Thailand Sihasak Phuangketkeow. Kuma dukkanin manyan jami’an biyu sun shaidawa Wang Yi, sabbin ci gaba da aka samu dangane da rikicin kan iyakar kasashensu, tare da bayyana aniyarsu ta sassautawa da dakatar da bude wuta.
A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, a matsayinta na kawa, kuma makwabciyar kasashen Cambodia da Thailand, Sin ba ta kaunar ganin sun tsunduma cikin yaki, tana kuma matukar takaicin rasuwar fararen hula sakamakon tashin hankalin da ya barke tsakaninsu. Ya ce a wannan karon, dauki-ba-dadi tsakanin sassan biyu ya tsananta sama da na lokutan baya, kuma idan hakan ya ci gaba, zai illata kasashen biyu, tare da gurgunta hadin kan kungiyar ASEAN. Daga nan sai ya bayyana cewa, matakin gaggawa da ya dace a dauka shi ne cimma matsaya, da dakatar da bude wuta cikin sauri, da dakile asarar da lamarin ke haifarwa, tare da sake gina amincewa da juna.
A daya bangaren, Prak Sokhonn da Sihasak Phuangketkeow, sun yi matukar jinjinawa matsayar Sin ta adalci, da kaucewa goyon baya bangare guda, da kokarinta na shiga tsakani, da ingiza tattaunawa, suna masu fatan Sin din za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ingiza matakan sassauta yanayin da gina zaman lafiya. (Saminu Alhassan)














