Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya yi kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da muguwar aniyarta ta sayarwa yankin Taiwan makamai.
Guo Jiakun, ya yi kiran ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, yana mai cewa Amurka ta yi gadarar bayyana shirin sayarwa Taiwan tarin makamai na zamani, wanda hakan ya keta hurumin manufar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwar hadin gwiwa uku, wadanda Sin da Amurka suka amincewa.
Jami’in ya kara da cewa, matakin na Amurka ya illata ikon mulkin kai, da tsaro, da ikon kare yankunan kasar Sin. Kazalika, matakin ya gurgunta yanayin zaman lafiya da daidaito a gabobi biyu na zirin Taiwan, tare da aikewa da sakon kuskure ga sassan ‘yan aware masu neman “‘yancin kan Taiwan”. (Saminu Alhassan)














