A ranar Alkiyama, bayan Annabi SAW ya bude kofar shiga Aljannah, Shahidai za su taho zuwa shiga Aljannah, sai a tambayesu, waye ya kira ku? Sai suce Malamai suka gaya mana cewa, mune farko, sai a ce musu, to kubari Malamai su fara shiga; Malamai da jin haka, sai su ta so za su shiga, sai a tambayesu, ku su waye? Sai su ce, mu ne Malamai, to ya aka yi kowa bai zama Malami ba sai ku kadai, sai suce, saboda duk sun tafi wurin neman abinci muka muna wurin koyon ilimi, to ku ba kwa cin abinci ne? Muna ci, wasu ne suka dauki nauyin cin abincinmu, to ku bari masu ciyarwa su fara shiga. Don haka, sai masu ciyarwa sun fara shiga Aljannah, sannan Malamai sannan Shahidai.
Annabi SAW, ya cewa Sahabbansa, shi ne mafificin mutanen farko da na karshe, ba alfahari ba!
- Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah
- Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
Jama’a mu tambayi kanmu mana, a ina Annabi SAW ke fadan wannan kirarin? A gaban sahabbansa ya ke fada musu waye shi. Wannan abu shi ake kira taron Maulidi.
16 – Baihaki ya fada a cikin falalar sahabbai da ya ruwaito cewa, sayyadina Ali amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya taho zuwa ga Annabi SAW, sai SAW ya ce, “Haza Sayyidil Arabi – ga shugaban Larabawa nan ya taho,” sai sayyada A’isha ta ce, “Alasta Sayyidil Arabi? – ba kaine shugaban Larabawa ba?” Sai Annabi SAW ya ce, “Ana Sayyidil alamina – ni shugaban halitta ne gaba daya.”
Saboda walitta, wadanda suka tara karatu, ba su bai wa sayyadina Aliyu hakkinsa ba, kowa ya san Sayyadina Ali waliyyi ne, don haka, babu wanda ya sha wahalar walitta irinsa. Ko a hannun ‘yan uwansa bai sha ba, ballantana kuma saura. Yana daga cikin wadanda suka tara ilimi, shugaban Larabawa, ya fi kowa iya Larabci, malami ne kum ga haddar ilimi. Annabi SAW ya ce, na roki Ubangiji ya sanya ayar “wata iyaha uzunun wa iya” ta zama kunnen sayyadina Ali, amma gaba daya, Hadisai 1,500 aka ruwaito daga gare shi, daga cikin hakanma, akwai Hadisi daya, an samo shi ta fuskoki 100, hakan na nuna cewa, Hadisai 100 sun koma 1. Hadisan ma ba na wani muhimmin ilimi ba, kamar wani hadisi da aka ce, sayyadina Ali ya nemi Mikdadu ya tambaya masa hukuncin zubar maziyyi a wurin Annabi SAW saboda yana jin kunya duba da auren ‘yarsa (Sayyada Fatima) da yake yi.
Mai littafin sharhin Nahjul Balaga, ibnu Abil hadid, ya yi sufuli 22, duk akan hikimomi da ilimai na sayyadina Ali. Shugaban Jami’ar Azhar, Muhammad Abdu, ya yi sharhi mai yawa akan wani ilimi da ke cikin Nahjul Balaga. To amma, wadanda suka tara ilimi, a ina suka baro hadisan sayyadina Ali? Saboda mafi yawancin wadanda suka tara ilimi, ba but kyakkyawar dangantaka tsakanin sayyadina Ali da kakanninsu. Akwai wani babba daga cikinsu, kullum sai ya tsinewa sayyadina Ali sau 79 da safe da yamma. Wadannan maganganu ba su da dadin fada amma dai karatu ne yazo da su.
Akwai mutanen da ake cewa, sun kai sayyadina Ali inda bai kai ba amma suna da maganganunsa littafi mai sufuli 111, duk hadisan sayyadina Ali ne aciki.
Anan za mu fahimci cewa, tunda sayyadina Ali shi ne shugaban Larabawa, to dole shi ne mafi fusaharsu, kuma Annabi SAW tunda shi ne shugaban halitta (kowacce kabila), don haka, shi ne mafi fusahar dan kowane yare.
Indai wannan Hadisin dake cewa, Sayyadina Ali shi ne shugaban Larabawa, ya inganta, sai ka samu Sayyadina Ali karshen ilimi.
17 – Mujahidu ya ruwaito, Manzon Allah SAW ya ce, “an bani abu guda biyar da ba a bai wa kowa ba kafin ni na daga Annabawa:
1 – An aiko ni zuwa jar fata da bakar fata, amma sauran Annabawa, iya ‘yar jama’arsa kadai, amma Annabi SAW, zuwa ga dukkan mutane.
2 – An sanya tsoro na a zukatan makiya na, duk makiya Annabi SAW, da sun ji an ce, ya taho sai su tsere.
3 – An halasta min ganima wacce kafin ni babu wanda aka halasta masa na daga Annabawa kafin ni.
4 – An bani ceto, sai na tanadar wa al’ummata, kuma in sha Allah za ta samu ceto ga wanda bai hada Allah da kowa ba.
5 – An sanya min kasa ko ina ta zama masallaci, kuma in babu ruwa, ta zama abin tsarki, duk inda Sallah ta riskeka, to nan ma masallaci ne, sai dai Malamai sun ce, banda makabarta, da bandaki mai kazanta, amma wanda yake tsaftatacce, ba ma zaka iya gane bandaki ba ne, ba laifi a yi ta nafilfilu aciki, da zikrai amma banda karatun Alkur’ani saboda girmamawa. A kowane yanayi kake, mutuwa na iya zuwa, babu wanda zai hana ka yin zikiri in mutuwa ta zo a wannan yanayi. Haka ma, a tsarin Darika, mace ba za ta karanta jauhara ba in tana haila amma za ta yi zikiri (La’ilaha illallah). Wani masani, da ake kira Aliyu Juma, ya yi fatawa cewa, mace ko tana haila za ta iya karanta Alkur’ani da ke cikin wayoyin hannu saboda ba Alkur’ani take tabawa ba a lokacin, idon wayar (screen) take tabawa. Malamai sun hadu cewa, in mace tana da haddar Alkur’ani, ko tana haila za ta iya yin Tilawarsa da kai amma ba tabawa ba.
Imam Malik, abu biyu sun rikita shi: Hadisan “La salata li jaril masjid illa fil masjid – babu sallah ga makwabcin masallaci sai acikin masallaci” da kuma Hadisin “ju’ilal arda kullaha masjidun – an sanya kasa ta zama ko ina masallaci,” Saboda shi ma makwabcin masallaci, gidan da yake, shi ma masallaci ne, yanzu ya za a yi? Imam Malik ya dauki tsawon shekaru bai yi fatawa kan hadisan nan biyu ba, in an tambaye shi, sai yace shi ma bai sani, har sai da wani Malami da ake kira Imamuz zuhuri ya ziyarce shi, sai ya ce masa na zo maka da wani hadisi, bayan ya zayyano masa Salsalar Hadisin, sai ya ce, Annabi SAW ya ce, “salatul jama’ati tafdilu salatul fazzi bi sab’i wa ishrina darajatan – salla acikin jama’a ta fifici sallar mutum daya da daraja ashirin da bakwai,” imam Malik sai murna ya yi waje wurin jama’a don shaida musu ya samu amsar fatawar hadisan nan da suka rikice masa. Ma’ana, makwabcin masallaci da ya yi Sallah shi kadai ba a masallaci ba, sallar shi tana nan sai dai bai samu ladan wanda ya yi salla tare da jama’a ba acikin masallaci. In ma ya yi Sallah tare da iyalinsa kamar ya yi sallah ne a masallaci tare da jama’a.
18 – Hakimit tirmizi mai hadisi, ya ce, duk sarki dole ya zama yana da kayan aiki irin na masarautarsa, ya zama yana da kudi da dai sauransu. Ana cewa, mabiya su ne masarauta, muridai su ne Shehunai. Ma’ana, da shugaban kasar da yake mulkar mutane 10 da wanda ke mulkar 11, wa yafi girman daraja? Yawan adadin mutanen masarauta, shi ne girman masarauta.
Kowane sarki, Allah yana ba shi kayan aiki ne irin na masarautarsa.
Manzon Allah SAW, cewa yake, “an aiko ni ga duk halitta: Asia, Russia, Afrika, Amurka, Turai…”, kuma kowacce nahiya da irin kwarewarta da iliminta kuma sai Annabinta ya yi mata daidai, ashe tunda haka ne, Allah zai tara wa Annabi SAW abubuwa masu yawa na daga hikima, ilimi, ma’arifa abun da bai bawa wanin Annabi SAW ba. Kuma hakan ce ta faru, har wasu ke ganin an cika masa abubuwa da yawa, an kai shi inda Allah bai kai shi ba. Ba haka ba ne, muƙamin na shi ne. Wanda ilimin shi ya fi, dole ya fi duk wanda yafi ilimi girman aji. Wani a firamare kawai zai iya karantarwa, wani zuwa Sakandare, wani zuwa Jami’a, wani kuma zuwa duk jami’o’in duniya. Annabi SAW, duk duniya babu mai ilimin shi don haka, shi na duk duniya ne! Amma kace, za ka auna Annabi da ‘yar iya wayewarka ta dan lungunku, ‘yar kwakwalwarka, hakan bai dace ba.
Don haka, Allah ya bai wa Annabi SAW matattarar ilimi, hikima da ma’arifa wanda bai ba wa waninsa ba. Ubangiji ya tattare duk wannan acikin ayar, “Fa’auha ila abdihi ma’auha – an bashi abin da aka bashi”, duk abin da za a gaya wa Annabi SAW bai kai wannan aya ba.
A wurin fasaha, Annabi SAW ya ce, an bani “jawami’il kalimi – an ba ni matattarar kalmomi”, malamai na wancan zamanin suke cewa, abin da ake nufi da haka shi ne, mu ce (Kibiya – abun da mata ke tsefe gashi, kuma abin da ake harba fari da gwafa, kuma magana ce. Hakan na nufin kalma daya amma tana da ma’anoni da yawa. A cewar Malaman wannan zamani, suna cewa, hadisin yana nufin, Annabi SAW an sanar da shi lissafe-lissafe da logarithms na sanin ilimin kowane harshe, da kowace halitta.
Don haka, Littafinsa ya tattare duk littattafai, al’ummarsa ma haka
18 – Muhammad bin Aliyu (Turmizi) ya fitar da hadisi acikin littafinsa ‘Nawadiru’, wanda ya karɓa daga Abi Hurairata (RA), Abi Hurairata yana cewa, Annabi SAW ya ce, “Ubangiji ya riki Annabi Ibrahim badadi, Annabi musa kuɓutacce (wanda aka tseratar), ni kuma ya rike ni masoyi”. Ubangiji ya yi rantsuwa da cewa, “na rantse da girmana da buwayata, sai na daura masoyina akan badadi lna da kuɓutacce na (Annabi Ibrahim da Annabi Musa)”.
19 – ya zo a Hadisin Muslim daga Abi Hurairata yana cewa, Annabi SAW ya ce, “Misali na da misalin sauran Annabawan da suka gabata, kamar misalin wanda ya gina gida ne ya cika komai amma sai ya bar wata kafa inda za a iya saka bulo daya, da za a saka bulo din da ginin gida ya cika daidai ba gibi. Kowa ya zo sai ya ce, gini ya yi kyau amma me yasa ba za a saka bulo daya a kulle nan ba? Annabi SAW ya ce, to ni ne bulo dayan nan! Don haka, Annabi SAW shi ne cikamakon halitta.
20 – Duk in Ubangiji zai kira sunan kowane Annabi A Alkur’ani, gundarin sunansa yake kira, amma don ya koya mana girmama Annabi SAW, sai ya hana mu kiransa da ‘Ya’ kuma ya gargademu a Alkur’ani da cewa, kada mu rika kiran Annabi SAW kamar yadda muke kiran junanmu (la taj’alu du’a arrasuli bainakum kadu’a’i ba’adikum ba’ada), za ka ji Kur’ani yana cewa, “ya Adamu, Ya Ibrahim, Ya Musa, Ya Yahya, Ya Zakariya”, amma a wurin Annabi SAW, sai dai kaji yana cewa, “Ya AyyuharRasul, Ya AyyuhanNabiyyu,”.
Har ila yau, don kada ace, Alkur’ani bai fadi sunan Annabi SAW, sai ya kama suna amma da girmamawa, kamar Muhammad Rasulullah, wama Muhammadun illa Rasulun, makana Muhammadun aba ahadin min rijalikum walakin Rasulullah,…














