A halin yanzu, ana shigar da hajojin da aka daukewa haraji masu dimbin yawa, cikin lardin Hainan na kasar Sin, ta tashar jiragen ruwan Yangpu, da ma sauran tashoshin da kasar Sin ke amfani da su wajen bude kofa ga kasashen waje.
Tun daga jiya Alhamis 18 ga watan nan, aka fara aiwatar da manufar kafa hidimar “kwastam mai zaman kanta, a duk fadin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin” a hukumance, wanda hakan ya nuna aniyar kasar Sin ta kara bude kofa ga waje ta hanya mai inganci, tare da kuma samar da sabbin damammakin cimma moriya ga kasashen duniya bisa bunkasuwar kasar Sin.
A jiya Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, matakin kaddamar da manufar kafa hidimar “kwastam mai zaman kanta, a duk fadin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin”, ta zama wani sabon matakin da aka kirkiro, wanda tabbas zai kafa tushen ci gaban lardin Hainan, gami da samar da damammakin raya harkokin kasuwanci ga jama’ar Sin, da na kasashen ketare.
A yayin taron manema labarai na wannan rana, Zakharova ta amsa tambayar da wani dan jarida ya yi mata, game da matakin kasar Sin na kafa hidimar kwastam mai zaman kanta a tsibirin ciniki maras shinge na Hainan, da yadda kasar ta kafa sauran yankunan gwajin ciniki maras shinge, inda ta ce hakan ingantattun matakai ne masu amfani na raya cinikayyar dake tsakanin sassan kasa da kasa, wadanda za su kyautata tsarin ciniki, gami da fadada hanyoyin cinikayyar waje.
Ta ce hukumomin kasar Sin da na kasar Rasha masu nasaba da batun, suna mayar da matukar hankali kan habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin gina yankunan raya tattalin arziki na musamman. (Mai Fassara: Maryam Yang)














