ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

RIGATA 2026: Al’umma Daga Ciki Da Wajen Nijeriya Za Su Baje Kolin Al’adun Gargajiya

by Bello Hamza
1 day ago
RIGATA

Al’ummar Masarautar Yauri da ke a kudancin Jihar Kebbi, sun shirya tsaf, domin gudanar da bikin gargajiya na Rigata da ake sa ran zai gudana a cikin farkon shekera mai kamawa .

An shafe sama da shekaru 200 ana gudanar da wannan bikin gargajiyar wanda kuma ba a ciki ganin irinsa, a kasar nan ba, saboda ana gudanar da bikin ne, kan tudu da kuma gudanar da wasanni, a kan Kogin Neja.

  • Babu Wani Annabi Mai Daraja Kusa Da Ta Muhammad Rasulullah (SAW)
  • Gwamnatin Kogi Ta Tabbatar Da Sace Mutum 13, An Kashe ’Yan Bindiga 4

Bikin na da nasaba da hudda a tsakanin ‘yan Adam da kuma dabbibin ruwa, kamar Dorinar ruwa, Kada wadanda suke ke kai wa bil Adama hari, tare da janyo mutuwar su.

ADVERTISEMENT

Domin a dakile wannan barazanar hakan ke sanya wa a duk shekara, jaruman Gungu, suke shiga cikin Kwale-Kwale dauke da makamai suna farautar irin wadannan mugayen dabbobin ruwan.

Suna kuma yin hakan ne, domin su samar da tsaro a kan Kogunna da tabbatar da zirga-zirga a cikin sauki da kuma kara habaka sauran hada-hadar kawuanci a Kogunan.

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

Bayan zuwa Turwan mallaka a karni na 19, an haramta farautar Dorinar ruwa, sai dai, daga baya, an ci gaba da yi a bikin na Rigata, domin a nuna irin karfin da Masarautar take da shi, musamman a lokutan bukukuwan aure.

Kai ziyarar da marigayi Sardaunan Sokoto kuma Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, a yankin na Yauri, hakan ya sake farfado da bikin na Rigata, wanda lokacin ziyararsa, aka gudanar da wasanni da kuma baje kolin amfanin gona, domin a karrama shi.

Bisa jajircewar Mai Martaba Sarkin Yauri Dakta Mohammad Zayyanu Abdullahi, CON, da kuma namjin kokarin gwamnan jihar, an sake farfado da bikin karo na 45.

Mayar da hankali da Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris kuma, Kauran Gwandu, Gamjin Yauri, ya taimaka matuka wajen farfado da martabar bikin.

Kazalila, tsarin da Gwamna Idris ya samar na daga darajar yawon bude Ido a jihar, hakan ya kara janyo ra’ayin bunkasar bukukuwan gargajiya a jihar.

Misali, manya bukukuwan gargajiya kamarsu, bikin kamun Kifi na kasa da kasa na Argungu da ake gudanarwa a garin Argungu,bikin gargajiya na the Uhola.

Bikin gargajiya na Zuru da ake yi a yankin Geandu, ya taimaka wajen daga darajar yawon bude Ido na Jihar Kebbi a Idon duniya.

Duba da yadda ake gudanar da manyan bukukuwan gargajiya a kasar, sai dai, akwai wasu manyan kalubale nan a ci gaba da gudanar da bukuwan da kuma karancin kudi, musamman domin a ci gaba da gudanar da bukukuwan.

Bukukuwa da dama, sun bace bat, saboda rashin kudin ci gaba da gudanar da su, wasu ma, tun daga matakin farkon fara gudanar da su.

Idan har ana son gudanar da bukukuwan gargajiya su ci gaba da dorewa, dole ne, alumma su bayar da na su goyon bayan, musamman wajen samar da kudade.

Bikin na Rigata, na daga cikin manyan bukuwan da ke a kasar ana kuma gudanar da bikin ne, a duk shekara a cikin watan Fabirairun.

Ana fara gudanar da bikin ne, ta hanyar baje kolin amfanin gona, sai kuma nuna al’adun gargajiya da kade-kade da kuma raye-raye, tare da yin gasar kokawar gargajiya.

A bikin ana gudanar da gasar wasa da Kwale-Kwale a kan Kogi, inda kuma a bikin ya hada da, ‘yan tawagar kai Amarya tare da yi mata rakiya da kade-kade a cikin Jirgin Kwale-Kwalen da aka yi masa ado

A shekarun baya, ana yi wa Amaryar rakia ne, zuwa gidan mijinsu a cikin Kwale-Kwale, musamman a yankunan da ake da Rafuka.

A yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bkin na bana, ‘yan Nijeriya na ci gaba da sa ido, domin su ga yadda bikin na zai gabatar da wasu sabbin dabaru, musamman a bangaren kade-kade.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
Ƴansanda Sun Tsaurara MatakanTsaro A Borno Gabanin Ziyarar Tinubu

Ƴansanda Sun Tsaurara MatakanTsaro A Borno Gabanin Ziyarar Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.