A jiya Juma’a bisa agogon wurin, a karon farko aka nuna jigo da tambarin shagalin murnar bikin bazara na shekarar 2026, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG zai shirya, a muhimman yankunan dake cibiyar birnin Moscow na kasar Rasha, inda aka nuna dukkanin tunanin kirkirar tambarin shagalin, da ma salonsa na gani da ido, wanda ya kunshi dawaki hadu da aka kawata su da alamomin gargajiya na Sin dake nufin “Ba za a iya dakatar da gudun dawaki ba”, wanda hakan ya ja hankalin tarin al’ummar wurin inda suka rika tsayawa suna kallo. (Bilkisu Xin)
ADVERTISEMENT














