Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano (MAAUN), ta fuskantar matsanancin bincike daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, kan harajin da ta kakaba wa daliban da ta yaye na kimanin naira 750,000.
Hukumar kula da jami’ar mai zaman kanta da ke Kano, ta tilasta wa daliban da ta yaye biyan wadannan makudan kudade, kafin bayar da sakamakon karshe da kuma tura sunayensu zuwa hukumar NYSC da kuma ba su sauran takardun da suka dace kafin yaye daliban, lamarin da ya sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shiga tsakani.
- Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- ‘Yan Wasa Biyar Da Tauraruwarsu Za Ta Haska A AFCON
Hukumar korafe-korafen da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, ta umarci jami’ar ta da dakatar da bukatar ta karbar Naira 750,000 daga hannun daliban.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 27 ga watan Nuwamban 2025, mai dauke da sa hannun shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Salisu Saleh, an umarci jami’ar da ta dakatar da karbar wadannan kudade tare da bai wa daliban takardar shedar tafiya bautar kasa (NYSC) da kuma takardar shedar kammala karatun jami’ar.
Hukumar ta bayyana a cikin wasikar cewa, tana daukar matakin ne daidai da ikonta a karkashin sashe na 9 da 15 na dokar PCACC ta 2008 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, 2010), da kuma hana ayyukan da ka iya kawo cikas ga binciken.
Hukumar ta tabbatar da samun korafi a hukumance game da sanya kudaden da kuma damuwar cewa, akwai barazanar hukunta daliban sakamakon kin biyan kudin.
Duk da umarnin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayar, iyayen daliban da aka yaye, sun koka da rashin mutunta sanarwar, kamar yadda hukumar gwamnati ta bayar, inda a maimakon haka jami’ar ta yi musu barazana.
Mahaifiyar dalibin da ya kammala karatun digirin da ya nemi a sakaya sunansa ya nuna damuwarsa kan yadda mahukuntan jami’ar suka rufe kofa tare da kin amsa tambayoyi daga iyayen.
Da yake mayar da martani game da karin korafe-korafen, Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Saidu Yahya, ya tabbatar da binciken da ake yi kan lamarin tare da tabbatar da aniyar ganin cewa; ba a cutar da kowa ba.
Binciken LEADERSHIP, ta tabbatar da cewa, hukumar jami’ar ta Maryam Abacha, ta samu izinin daga kotu na dakatar da binciken hukumar korafe-korafen ta Jihar Kano kan al’amarin, har sai ta kammala bincikenta tare da yanke hukunci.
Har izuwa lokacin hada wannan rahoto, ba mu samu damar jin ta bakin hukumar jami’ar ta MAAUN din ba.













