Ministan Muhalli a Nijeriya Balarabe Abbas Lawal ya bayyana irin yadda sarakunan gargajiya za su bada gudunmawa wajen dakile barazanar kwararowar hamada a Nijeriya.
Ministan muhalli yana magana ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma fadar mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman domin neman shawarar irin ta iyaye sarakuna.
- Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
A cewar ministan Muhalli Hon. Balarabe Abbas sun zo Katsina ne domin gudanar da babban taron muhalli wanda aka saba shiryawa duk shekara inda a bana za a gudanar da shi a Katsina.
Ya kara da cewa wasu daga cikin jihohin arewacin Nijeriya ciki harda Katsina suna fuskantar barazanar muhalli da canjin yanayin wanda ya zama kalubalen a duniya baki daya.
Haka kuma ya kara da cewa daga cikin irin abubuwan da za su maida hankali a wannan taron na shekarar 2025 shi ne, rage sare itatuwa ba tare da an shuka wasu ba wanda ya ce hakan na taimakawa wajen gurbatar yanayi a duniya.
“Abinda muke so yanzu shi ne, gwamnati ta fito da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen rage yadda ake amfani da itatuwa wajen yin girki ba tare an shuka wasu ba da kuma irin hadarin da mata ke fuskanta a ya yin girki da itatuwa a wannan zamani.’ inji shi
Ministan Muhallin ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da wasu sabbin shirye-shirye na maye gurbin amfani da itatuwa wajen yin girki inda za ta samar da wasu sinadarai da za a rika amfani da su don kaucewa dumamar yanayi
Haka kuma ya bayyana cewa idan ta kama sai an sare itatuwa to ana bukatar a shuka guda uku duk inda aka sare guda daya wanda haka zai taimaka wajen bunkasar yanayin mai kyau da al’umma zata amfana da shi wajen samun kyakkyawan yanayi.
Hon. Balarabe Abbas wanda ya ce duk wata nasara da ake bukata dole ne a sanya iyaye sarakuna saboda tasirin su a cikin wannan al’umma.
Da yake jawabi mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi na’am da wannan taro wanda ya ce ya yi daidai da halin da al’umma suke ciki na rashin kula da muhallinsu
Sarkin na Katsina ya bada tabbacin goyon bayan masarautar da wajen ganin an cimma nasarar wannan gagarumin aiki na tabbatar da samun kyakkyawar muhalli wanda ya ce muhalli shi ne rayuwa.
Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce al’umma ta rasa wadanda za su yi masu jagoranci wajen ganin an kyautata muhallin da ke tafiyar da rayuwar al’umma a kowane lokaci da kuma zamani.













