Za a buɗe gasar kofin Nahiyar Afrika (AFCON) na 2025 da TotalEnergies zai ɗauki nauyi a hukumance a daren Lahadi da wani gagarumin bikin buɗewa da aka shirya gudanarwa da ƙarfe 6:00 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, ƙasar Morocco. Bikin zai kasance wata guda na ƙwallon ƙafa da bukukuwan al’adu a faɗin nahiyar Afrika.
Fitaccen mawakin Afrobeats daga Nijeriya, Davido, na daga cikin manyan taurarin da za su nishaɗantar da jama’a a bikin buɗe gasar. Mawaƙin ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X yana nuna shi da tawagarsa sun isa filin wasan, lamarin da ya ƙayatar a kafar sada zumunta. “Zan yi waƙa a bikin buɗe AFCON! 6:30 na yamma WAT,” in ji Davido.
- Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey
- AFCON 2026: ‘Yan Wasa 10 Da Suka Isa Sansanin Super Eagles Zuwa Yanzu
Sauran mawaƙan da za su halarci bikin sun haɗa da French Montana, da Douaa Lahyaoui, da Lartiste da Says’z, inda ake sa ran za su ƙara wa bikin armashi. Haka kuma, fitattun mawaƙan Afrika irin su Angélique Kidjo, da Jaylann da L’Artiste za su gabatar da waƙar AFCON ta 2025, wadda ke ɗauke da saƙon haɗin kai da alfaharin nahiyar Afrika.
AFCON 2025, shi ne karo na 35 a tarihin gasar, zai gudana har zuwa 18 ga Janairu, 2026, inda ƙasashe 24 za su fafata a birane shida na Morocco. Masu shirya gasar sun bayyana cewa wannan zagaye zai kasance haɗin gwuiwar wasanni da al’adu, tare da nuna bajintar Afrika a fili da bayan fage.














