‘Yan Nijeriya 183 suka mutu a sanadiyar zazzabin Lassa da Shawara,yayin da kuma mutane 1,650 suka kamu a Jihohi 36 da Babban birnin tarayya Abuja.
Cibiyar hana yaduwar cututtuka da maganinsu ta kasa NCDC ta bada bayanin halin da ake ciki dangane da cutar zazzabin Lassa abinda ke nuna cewar ta bazu sosai a Nijeriya,inda mutane 6,471 suka kamu da ita.
- Za Mu Iya Ciyar Da Kifayen Da Muke Kiwo Da Mushe?
- ‘Muna Kira A Samar Da Jami’an Tsaro Na Yankin Arewacin Nijeriya’
Wannan kuma a kananan hukumomi 101 ne daga Jihohi 25, mutane 169 ne suka riga mu gidan gaskiya.
Har ila yau cibiyar ta ce mutane1,179 sun kamu da cutar Shawara a kananan hukumomi 416 a Jihohi 36 da Babban birnin tarayya Auja, wannan cut ace da tayi sanadiyar mutuwar mutane 14 daga Jihohi 10.
Rahoton ya kara da cewar yawan wadanda suka kamu da cutar zazzabin Lassa ta karu idan aka yi la’akari da abinda ya faru a shekarar 2021.
Ta ce mutane 899 ne suka kamu daga cikin 6,471 da ake sa ran sun kamu da ita, wanda kuma wadanda sabbin da suka kamu da cutar suka ragu daga 6 zuwa 5 a mako na 34 a shekarar 2022.
Rahoton ya kara da cewa wadanda suka kamu da cutar kashi 70 daga Jihar Ondo ne, 31 Edo, sai kuma Jihar Bauchi na da kashi 13 cikin dari, wadanda suka kamu da cutar daga shekara 21 ne zuwa 30.
“Bugu da kari daga mako na 1 zuwa na 34,a shekarar 2022,an samu rasuwar mutane 169 da aka samu sun kamu da cutar,wannan shi ya bada kashi 18.8, wannan bai kai na shekarar 2021 ba duk a irin wannan lokacin, domin ya kai har kashi 22.7.
“A mako na 34,sai sababbin wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar suka ragu daga daga 6 zuwa 5 a cikin makon,an samu wannan rahoton ne a Jihohin Ondo da Edo.
Wannan daga Jihohin Ondo da Edo ne.
“Gaba daya a shekarar 2022, Jihohi 25 sun samu a kalla mutum 1 daya kamu da cutar a kananan hukumomi 101 kmar yadda rahoton ya bayyana’.
Ita ma cutar Shawara kamar yadda cibiyar hana yaduwar cutttuka da maganinsu ta kasa ta bayyana, Jihohin Borno,Jigawa da Katsina sune suka bada rahoton wadanda suka kamu sun hada da 100, 81 da 81,yayin da kuma Legas ita ke da mafi rashin yawa na mutane 4 da suka kamu da cutar Shawara.
Rahoton ya nuna daga cikin1179 da ake sa ran sun kamu da cutar daga1 ga watan Janairu zuwa 31 Agusta 2022,an samu mutuwar mutane14 Abia (1),Bayelsa (1), Benuwe (1), Imo (1), Kaduna (1),Katsina (2), Kebbi (1), Taraba (2), Yobe (1) sai kuma Jihar Zamfara (3).
“Gaba daya daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Yuli 2022, daga cikin 1179da suka kamu da cutar Shawara daga kananan hukumomi 416 Jihohi 36 da Babban birnin tarayya Abuja kamar yadda rahoton ya bayyana.
An gano kashi 74 na wadanda suka kamu da cutar shekarunsu daga 30 zuwa kasa da haka, inda kuma166 (kashi 10)1179 an diga masu rigakafin maganin allurar cutar Shawara.