Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a ranar Lahadi da Litinin za a sauko da tutar kasar kasa, da kuma a ofisoshin jakadancin kasashen waje domin nuna girmamawa ga Sarauniyar Ingila, Elizabeth II wacce ta rasu a ranar Alhamis.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin kasashen waje ta fitar, ta ce Sarauniyar ta ”Nuna kwazo a tsawon lokacin da ta shafe a kan karagar mulkin Birtaniya, kuma shugabar Kungiyar Kasashe Rainon Ingila.
- Manyan ‘Yan Majalisar Birtaniya Sun Yi Mubaya’a Ga Sabon Sarki, Charles
- Neman Illata Kasar Sin Ya Haifar Da Matsalar Tattalin Arziki Ga Amurka
”Haka kuma ta nuna jajircewa wajen wanzuwar zaman lafiya da hadin kai tsakanin kasashe” in ji sanarwar.
Tuni dai gwamnatin Nijeriya ta mika sakon ta’aziyyarta tana mai cewa Birtaniya da Njeriya sun kasance cikin kyakkyawar dangantaka karkashin mulkin Sarauniyar.
Nijeriya ce dai kasa mafi girma a Afirka da Birtaniya ta taba yi wa mulkin mallaka.
Tuni dan Sarauniya Elizabeth, Charles George III ya zama sabon Sarkin Ingila.