A yanzu haka, mutum tara ne aka tabbatar wani Bene mai hawa daya ya rufta da su a yankin Maryland dake jihar Legas.
Kakakin Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA na shiyyar Kudu Maso Yamma, Ibrahim Farinloye, a sanarwar da ya fitar ya ce, labari ya isowa hukumar cewa, wani Bene mai lamba 47 a titin Akinwunmi a Maryland, Ikeja ya rufta da Mutum Tara.
Ya ce, ruwan sama da aka yi kamar da Bakin Kwarya a safiyar ranar Litinin ne ya haifar da ambaliyar da ta barke zuwa wasu Unguwannin da ke jihar.
Wata da ta tsallake Rijiya da baya mai suna Blessing ta ce, Mutum tara ne a cikin ginin akasarin su mata ne.
Mai gidan ya samu tsallakewa, ta hanyar Tsani, inda a yanzu haka, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, LASEMA da ‘yansanda suka bazama wajen ceto Rayuwar sauran mutanen Tara.