Assalamu alaikum ‘yan uwa barkanmu da war haka, sannunmu da arzikin sake haduwa a wannnan fill namu mai albarka RAINO DA TARBIYYA. Yau filin zai yi tsokaci ne a kan koyawa yara zaman lafiya da kowa. Yana daga cikin zabi’a mai kyau yaro ya tashi yana muamala mai kyau kuma yana zaune lafiya da kowa, hakan ba zai faru ba har sai in an koya masa daga guda.
Iyaye mu kula sosai wurin ganin mun dora yaranmu akan zaman lafiya da mutunta al’ umma. Idan muka sake ba mu sa ido wurin koya musu yadda za su zauna da kowa lafiya ba to a karshe yaro zai tashi ya zama marar ji da rashin mutunta mutane a cikin al’umma,wanda hakan zai jawo masa koma baya a dukkanin al’amuransa na rayuwa.Wasu iyaye kan bada gudumawa wurin kyale yaro kara zube ba tare da tsawatarwa ba a lokacin da take neman rigima a bari.
Zamani ya so da sauye sauye wanda tilas sai ana duba wannnan bangaren na koya wa yaranmu yadda za su sauna da kowa lafiya cikin mutuntawa da girmamawa koda kuwa yare gari addinin ba daya ba,hakan zai sa yaro ya tashi da sanin kima da darajar dan ‘Adam duk daga inda ya fito.
Allah ya ba mu ikon gyarawa.