Bayan tashi taro bararn-baran na Gwamnonin jam’iyyar APC da ya gudana jiya Litinin a Abuja, gwamnonin sun mika wa Shugaba Buhari sunayen ‘yan takarar shugaban Kasa na masalaha biyar da suke so ya zaba aciki.
Jaridar Aminiya ce ta tabbatar da rahoton, inda ta ce Gwamnonin sun mika sunayen ne da sanyin safiyar Talata.
Sunayen, a cewar majiyar sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu;Â Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi; Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi.
Gwamnonin, a yayin zantawarsu da shugaba Buhari, sun yi alkawarin komawa Fadar Shugaban Kasa bayan sun tattauna da Kwamitin Zartarwar jam’iyyar na kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp