Yau Alhamis, ’yan sama jannati 3 na kasar Sin da ke aiki a tashar sararin samaniyar kasar Sin sun yi wa matasa da kananan yara na gida da wajen kasar Sin fatan alheri ta kafar bidiyo ta bakin CMG.
Yara da matasa daga kasashe daban daban sun halarci gasar zane-zane dangane da mafarkin sararin samaniya da tattaunawa a tsakaninsu da ’yan sama jannati na kasar Sin.
Madam Liu Yang, daya daga cikin wadannan ’yan sama jannatin 3 ta yaba wa zane-zanen, tana mai cewa, an fahimci sha’awar matasa da kananan yara kan sararin samaniya da kuma burinsu na zuwa sararin samaniya kamar yadda tsuntsaye suke yi.
Zane-zanen sun shafi yawon shakatawa a sararin samaniya, yin wasa da takwarorinsu masu launuka daban daban da ke zaune a duniya ta daban, da yadda ’yan sama jannatin 3 suka tashi zuwa sararin samaniya cikin kumbon Shenzhou-14. Zane-zanen na da kyau sosai.
Cai Xuzhe, dan sama jannati na daban ya kuma amsa tambayoyi masu ban mamaki da aka yi masa dangane da rayuwarsu da ayyukansu a sararin samaniya.
’Yan sama jannatin na kasar Sin sun gayyaci matasa da kananan yara a sassan duniya da su ziyarci tashar sararin samaniyar kasar Sin a nan gaba.
Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da gidan nune-nunen kimiyya da fasaha na kasar Sin, sun shirya gasar zane-zane dangane da mafarkin sararin samaniya da tattaunawa a tsakaninsu da ’yan sama jannatin daga watan Yunin bana, inda matasa da kananan yara daga kasashe da yankuna fiye da 20 suka gabatar da zane-zane fiye da 600 da tambayoyi fiye da dubu 1 dangane da sararim samaniya. (Tasallah Yuan)