‘Yan siyasa sun amince da cewa, kudi na da matukar muhimmanci a wajen samun nasara ko rashinta a yayin da suka tunkari zabuka a Nijeriya. Kawar da kudi a harkokin siyasar Nijeriya wani abu ne da ba zai taba yiwu ba gaba daya, dalilin haka kuma ba shi da wahalar ganewa.
A ‘yan shekarun nan an amince da cewa, ‘yan siyasa masu hannu da shuni sune a kan gaba a fafutukar kama madafun iko, yana iya kasancewa ne ko sun fito ne a matsayin masu takara kai tsaye ko kuma suna daukar nauyin wanda da yake takarar, saboda tsananin tasirin kudi a harkokin sisayar da ake fuskanta a 2023 wanda bashi da kudi ba a sa shi a cikin masu iya lashe zaben.
Tabbas tasirin kudi a harkokin siyasa lamari ne da bai tsaya a iyaka fagen siyasar Nijeriya ba, don ko a kasashen da suka cigaba harkar siyasa abu ne da yake da tsadar gaske kuma kudi na da tasiri kwarai da gaske. Amma bambanci da ake samu a tsakanin yanayin siyasar Nijeriya da ta kasashen da suka cigaba shi ne a can doka ta amince ‘yan jam’iyya da manyan kamfanoni su samarwa jam’iyya kudaden tafiyar da harkokinta na yakin neman zabe amma kuma dokar ta kayyade iyakar kudaden da za a iya kashewa, don kada a wuce gona iri. Amma ba haka abin yake ba a Nijeriya, don kuwa kafin wani dan siyasa ya fara yunkurin fara neman takarar kujerar gwamna ko ta shugaban kasa dole ya zamana yana da karfin samarwa da jam’iyyarsa kudi akalla kashi 80 na kudaden da ake bukata don tafiyar da harkokin da suka shafi jam’iyyar gaba daya, harkoki da suka hada da kudaden yakin neman zabe da sauransu. A wasu wuraren ana kashe kudaden ne ta hanyar daukar nauyin ‘yan jam’iyya masu zirga-zirgar tallata manufofi da akidun jam’iyyar a cikin mazabar mai takarar don jawo hanlakin masu zabe su zabe shi.
Amma ba haka abin yake ba a Nijeriya saboda tsananin talaucin da ake fuskanta yana da matukar sauki a sayi masu kada kuri’a a sassan Nijeriya. Rahoton Bankin Duniya na shekarar 2022 ya nuna cewa, wadanda suke a matsayin talauci sun kai mutum miliyan 95.1. abin da hakan ke nufi shi ne, tasirin kudi a siyasar Nijeriya zai cigaba da karuwa ne ba kakkautawa.
Idan za a iya tunawa a ranar Talata ce shugaban kasa Muhammadu Buhari a taronsa da Gwamnonin Jam’iyyar APC ya bayyana cewa, gwamnati ba za ta bari wasu masu rike da madafun iko su wulakanta ko yen barazana ga ‘yan Nijeriya ba a zabukan da ke tafe a 2023.
“Ba za mu amince wani ya yi amfani da kudadensa ko matsayinsa wajen yi wa al’umma barazana ko wulakanta su ba ta kowacce hanya. Wannan shi ne irin shugabanci da muke bukatar samu don ya cigaba daga inda muka tsaya. Nan da wata shida ‘yan Nijeriya za su tabbatar tare da godewa gwamnatin APC saboda a lokacin za su fahimci yadda muka gudanar da harkokin gwamnati cikin gaskiya da rikon amana,’’ in ji shi.
A halin yanzu ana samun kwarin giwa a kan yadda wasu Malaman addini ke kokarin yaki da yadda ake amfani da kudi a siyasar Nijeriya ta hanyar kin karbar kyautar kudi daga ‘yan siyasa. Kwanaki ne aka yi wani dan ‘yar takaddama a wani cocin Katolita da ke Jihar Kross Ribas inda wani Rabaren Dan Taratsi mai suna Rabaren Dakta John Ebele Ayah, Bisahap na yankin Uyo ya ki karbar kyautar makudan kudade daga Gwamna Ben Ayade.
Lamarin ya faru ne a Cocin St. Patrick da ke Ikot Ansa, Calabar, iyayin bikin nuna godiya a kan nada Maishari’a Emmanuel Agim Akomaye a matsayin Maishari’a a kutun Koli, Ayah ne ke jagorantar zaman addu’ar sai Gwamna Ayade ya sanar da bayar da tallafin Naira Miliyan 25 ga cocin a madadin ‘yalasa da gwamnati, nan take Bishap din ya karbi abin magana ya bayyana wa Gwamnan kin karbar kyautar, ya nemi Gwamnan ya yi amfani da kudaden wajen biyan ma’aikata albashin da suke bin gwamnati, wanna matakin ya samu yabo kwarai da gaske, mutane na ta yabo da Allah san barka”
Haka kuma kwanakin baya ne wani Malamin addnin kirista a garin Nsukka ya yi watsi da kyautar Naira Miliyan 10 da wasu shugabanin jam’iyyuar PDP suka bashi don ya goya musu baya a zaben da ke tafe a 2023.
Haka kuma idan za a iya tunawa wasu kungiyoyin addnin musulunci 2 sun yi watsi da kyautar Dala Miliyan 3 da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya basu don su goya masa baya a zaben 2015.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne, lallai wannan wasu halaye ne da ya kamata a yi koyi da su, musamman ganin wadannan hali na neman ba Malaman addini kudade wani kokari ne na ruruta wutar rikicin addini da na kabilanci a fadin kasar nan, saboda haka yakamata a nisanci wuraren ibaba da irin wannan kazantar.
A halin yanzu sabbin matakai da hukumar zabe ta (INEC) ta bullo da su, kamar aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura mai kwakwalwa da amfani da na’urar BIBAS zai kawo karshen magudin zabe da suka hada da sace-sacen akwatin zabe da dangwala kuri’a barkatai.
Amma kasancewar, yan siyasar Nijeriya da wayon gaske har sun samar da sabbin hanyoyin kaucewa doka, inda a halin yanzu suke sayen kuri’ar gaba daya kai tsaye daga masu kada kuri’ar. Wannan matsalar tana shafar mutuncin Nijeriya saboda haka ya kuma zama dole a dakatar da sayen kuri’a, ya zama dole a hukunta dukkan wadanda aka kama suna sayen kuri’a a zaben da aka yi a Jihar Osun ba tare da bata lokaci ba don ya zama darasi ga sauran masu niyyar aikata irin wannan halin a zabukka na gaba.
A yayin da Nijeriya ke kara dumfara zaben shugaban kasa a 2023 muna kira ga ‘yan Nijeriya su zabi shugabanni masu nagarta wadanda za su iya kai kasar nan tudun muntsira.