- Mutum 300 Suka Mutu -NEMA •NiMet Ta Yi Hasashen Karin Ruwan Sama
- Za Mu Tallafa Wa Wadanda Suka Jikkata -Gwamnati
Masana sun bayyana cewa, dumamar yanayi a duniya ya haifar da canje-canje na yanayi a wasu sassan duniya, wanda hakan ya kara ambaliyar ruwa a wasu sassan SDuniya, abin da ya kai ga asarar rayuka da duniyoyin al’umma.
Tabbas canjin yanayin da ake fuskanta a wannan lokacin yana faruwa ne saboda yadda al’umma ke karan tsaye ga muhalli wanda hakan kuma yana jirkita yadda yanayi ke tafiya har ya kai ga haifar da matsaloli irinsu tsananin yawan ruwan sama, ambaliyar ruwa fari da sauransu. Masu bincike sun nuna cewa, an samu karin fiye da kashi 50 a cikin cdari na yawan ruwan sama da ake samu a sassan duniya.
Bayan fuskantar Ruwan sama marka-marka a watan Agusta abin da ya haifar da ambaliyar ruwa a sassan Arewacin Nijeriya, Hukumar Kula da Yanayi NiMet ta kara gargadin cewa, wannan watan na Satumba ma akwa yiwuwar fuskantar Ruwan sama mai tsanani a wasu sassan yankin Arrewa wanda hakan na iya haifar da ambaliyar ruwa a wasu jihohin Nijeriya 20, jihohin da NiMet ta ankarar da su sun hada da Kebbi, Jigawa a yankin Arewa maso Yamma da Jihohin Borno, Bauchi da Taraba a yankin Arrwa maso Gabas, yayin a yankin Arewa ta tsakiya a kwai Jihar Filato. Sauran jihohuin da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a wannan wata na Satumba sun hada da Jihar Bayelsa a yankin Kudu maso Kudu.
Sauran jihohin sun hada da Kano, Adamawa, Ribas, Akwa Ibom, Kros Ribas, Abia, Imo, Inugu, Legas, Ogun, Osun, Ondo, Oyo da kuma Jihar Ekiti.
Hukumar ta bayyana cewa, an yi wannan gargadin ne tare da la’akari da yadda aka fuskanci yanayin ruwa a kasar nan a watan Agusta.
Sanarwar haka ta fito ne daga bakin jam’in watsa labarai na hukumar, NiMet, Muntari Ibrahim, ya kuma kara da cewa, ”Ruwan da aka tafka a watan Yuli da watan Agusta zai dora wasu nauyi a watan Satumba inda zai kai ga samun ruwa marka-marka abin da zai kuma haifar da ambaliya a sassan Arwacin Nijeriya. Sanarwa ta kuma kara da cewa, an samu Ruwan sama da ya kai awo 300mm a watan Agusta a jihohin Sokoto, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Kano, Borno, Gombe da Nasarawa wanda ke nuna hakan ya kai kashi 40 cikin dari ke nan na abin da ya kamata a samu, wanda hakan ya riga ya cika manyan rafukan yankin, inda ruwan da za a samu a watan Satumba zai kai ga haifar da ambaliyar da za ta iya mummunan barna a watan Satumba.
A kan haka NiMet ta shawarci Hukumomin bayar da Agajin Gaggwa na jihohi (SEMAs) su tabbatar da samar da hanyoyin kai agajin gaggawa tare da fadakar da al’ummar yankin domin rage irin illar da hakan zai kai ga hairfarwa in an samu ambaliyar ruwa awuraren da aka ayyyana.
Barnar da ambaliyar ta yi a wasu sassan Arrewa a watan da ya gabata suna da yawan gaske, an samu rasa rayuka da dukiyoyi masu dinbin yawa, filayen noma masu yawa sun salwanta abin da ya jefa al’umma da dama cikin halin ni’yasu.
Ambaliyar Ta Kashe Mutum 372 A Jihohi 33 Da Abuja Cikin Wata 8
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa NEMA, Mustapha Habib ya sanar da cewa, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 372 a jihohi 33 ba yankin babbar birnin tarayya Abuja a cikin wata 8 da suka gabata.
Ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da kayan aikin ceto na musamman da hukumar ta samar don fuskantyar ceto wadanda matsalar ambaliyar ruwa a sassan kasar nan ta shafa, ya ce, jihohin da suka fi fuskantar matsalar ambaliyar sun hada da Adamawa, Jigawa, Taraba, Kano, Bauchi, Nija, Anambra da Ebonyi.
Ya kara da cewa, a kan haka hukumar ta samar da kayan aikin ceto don saukaka ayyukan ceto al’umma in an samu ambaliyar, kayyakin sun hada da asibitin tafi da gidanka 3, kananan jiragen ruwa 3, jiragen ruwa na musamman don ceto mutane 2, kwalewkale don kai dauki, 2, kwalekwale na musamman, 3, tochila mai karfin gaske, 9, kamara na musamman, 15, da sauran kayayyakin da za a iya amfani da su don ceto al’umma a yayin da aka samu ambaliyar ruwa a sassan Nijeriya.
Sakamako ruwan sama masu nauyi tare da iska mai karfin gaske da aka sheka a sassa daban-daban a 2022, ya jawo ambaliyar ruwa mai tsananin gaske a fadin Nijeriya, yayin da wannan mummunan ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar mutuwar Yan Nijeriya kimanin 115.
Bugu da kari kuma, rahoton ya bayyana cewa kimanin ‘yan Nijeriya sama da 73,370 ne suka rasa muhallin su tare da karin wasu mutum 277 wadanda ambaliyar ruwan ya raunata, kana tare da karin wasu kimanin mutum 500,000 wadanda ibtila’in ya jefa cikin kuncin rayuwar; inda ya rusa dubban gidaje, gadoji, gonaki da sauransu.
A cikin wani rahoton da Ofishin Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ke samu lokaci bayan lokaci dangane da ambaliyar ruwan, wanda babban mai bai wa Fadar Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labaru, Mallam Garba Shehu ya sanya hannu tare da shan alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa yankunan da ibtila’in ambaliyar ruwan ya shafa a fadin kasar nan.
Shugaba Buhari ya bukaci daidaikun al’umma da kungiyoyin jinkai su tallafa wa dubban al’ummar da ambaliyar ruwan ya shafa domin rage musu radadin ibtila’in, kana kuma ya shawarci jihohi da kananan hukumomi a fadin Nijeriya su yi takamamen shiri wajen tunkarar wannan kalubalen da al’umma suka fuskanta.
Rahoton Fadar Shugaban kasar ya lissafa wasu daga cikin jihohin da ambaliyar ruwan ya yi ta’adi, wadanda suka hada da Lagos, Yobe, Borno, Taraba, Adamawa, Edo, Delta, Kogi, Niger, Plateau, Benue, Ebonyi, Anambra. Sauran su ne Bauchi, Gombe, Kano, Jigawa, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Imo, Abia hadi da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A wata kididdigar da gwamnatin Nijeriya ta bayar, ambaliyar ruwan ta barnata tare da rusa kimanin gidaje 37,633 a sassa daban-daban na kasar nan.
Kafin hakan, Shugaban Hukumar Bayarda Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA), Mista Mustapha Ahmed ya yi gargadin cewa hukumar ta yi hasashen cewa kimanin jihohi 32, tare da kananan hukumomi 233 zasu fuskanci barazanar ambaliyar ruwa a 2022.
Ya bayyana hakan ne a wani taron karawa juna sani wanda Hukumar ta shirya a watanin baya a Abuja, domin matakan kan-da-garki dangane da matsalolin ambaliyar ruwa. Taron masu ruwa da tsakin ya tattauna samar da hadin gwiwa tare da aiki tare wajen daukar matakan gaggawa kan kalubalen ambaliyar ruwan.
Ya kara da cewa, “Wannan ya biyo bayan rahoton hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta ‘Nigerian Meteorological Agency’ (NiMet) tare da sakamakon Hukumar ‘Nigeria Hydrological Serbices Agency’ (NIHSA) suka bayar dangane da hasashen abkuwar ambaliyar ruwa a 2022. Wanda ya zama dole mu dauki ingantattun matakan da suka dace.”
“Har wala yau kuma, mun aike da wasukun bayar da shawara da taswirorin yankunan da hasashen ambaliyar ruwan zai shafa a jihohi daban-daban zuwa ga gwamnatocin jihohin hadi da wasu kananan hukumomin da ibtila’in zai shafa kamar yadda hasashen Hukumar NIHSA ya nuna.” In ji shi.
Kano Da Jigawa
Jihohin Kano da Jigawa, ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar mutuwar kimanin mutum 50 tare da raba karin wasu sama da mutum 8,000 daga gidajen su, kana da lalata gidajen jama’a da jawo asarar miliyoyin naira, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a jihar (SEMA) ta bayyana inda ta yi karin haske da cewa ambaliyar ta katse gadoji biyu a jihar.
Kananan hukumomin da al’amarin ya fi kamari a jihar sun hada da Sankara, Karnaya, Birnin Kudu, Ringim, Dutse, Gwaram. Yayin da ruwan ya ruguza babbar gadar Birnin-Kudu, hanyoyin da suka hada garuruwan Babura, Garki, Kazaure, Gwiwa, da Yankwashi. Haka kuma ambaliyar ruwan ya datse hanyar Birnin Kudu zuwa Bauchi.
A wani rahoton da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayar, ya nuna yadda ambaliyar ruwan ya shafi kimanin garuruwa 225 dake kananan hukumomi 31 a jihohin Kano da Jigawa a cikin makonni 8- kamar yadda Ko’udinatan Hukumar mai kula da wadannan jihohin; Mallam Nuradeen Abdullahi ya bayyana.
A jihar Kano, ya ce kananan hukumomin sun hada da Tudun Wada, Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta, Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono, Tsanyawa, Rimin Gado da Dawakin Kudu.
A jihr Jigawa, kuma sun kunshi Kafin Hausa, Malam Madori, Hadejia, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun, Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Kaugama, Babura, Gwaram, Dutse da Kirikasamma.
Har wala yau da barnar da ambaliyar ruwan ta yi wa yan kasuwar Kantin Kwari, wanda ya jawo asarar miliyoyin naira tare da lalata shaguna sama da 250 a birnin na Kano.
A rahoton da SEMA a jihar Kano ta bayar, ya bayyana yadda ambaliyar ruwan tayi sanadiyar mutuwar kimanin mutum 9 da lalata gidajen jama’a sama da 6,417 da asarar sama da naira miliyan 500 a wannan daminar.
Wani mazaunin garin Birnin Kudu mai suna Alhaji Hassan ya bayyana wa Wakilinmu cewa, kauyukan da ambaliyar da fi shafa sun hada da Ringim, Auyo, Karnaya, Dahgoli, Gambara, jawun Tdu da kuma Hayin Malam, ya kuma ce, an tabbatar da mutuwar akalla mutum 50 da kuma rushewar gidaje fiye da 2000.
Alhaji Hassan ya kuma ce, hukumnar Bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA ta yi nata kokarin na tallafa wa al’ummar da iftila’in ya shafa don rage musu radadin da suka shiga.
Sakkwato Da Kebbi
Jihohin Sokoto da Kebbi, suma al’amarin bai canja zani ba inda ambaliyar ruwan ta wanda a karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, kimanin gidaje 350 ne suka rushe a yankuna uku- Shiyar Ajiya, Makera da Runji, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Yayin da Hukumar SEMA a jihar Kebbi ta bayyana cewa kimanin mutum biyu ne suka rasa rayukansu ta dalilin ambaliyar ruwan, kana gidaje 1000 suka ruguje a kananan hukumomi 6- Birnin Kebbi, Jega, Shanga, Koko/Besse, Ngaski da Arewa a jihar.
Borno Da Yobe
Jihohin Borno da Yobe, ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafi kananan hukumomi masu yawa a jihar Yobe tare da jawo asarar rayuwa da dukiya da miliyoyin naira a kananan hukumomin Bade (Gashu’a), Damaturu, Fika, Geidam, Karasuwa, Machina, Nguru, Potiskum da Yusufari. Al’amarin da yafi kamari a kananan hukumomin Gujba, Gulani da Tarmua da ruguza gadar Katarko. Bugu da kari kuma ta barnata amfanin gona da lalata gidajen jama’a.
A jihar Borno, ambaliyar ruwan ta shafi yankuna 11 a kananan hukumomin Jere, Monguno da Kala Balge a jihar. Wanda ya shafi kimanin mutum 1317 tare da jawo asarar miliyoyin naira a jihar.
4. A jihar Nija, kimanin mutum 8 ne suka gamu da ajalinsu ta dalilin ambaliyar ruwan da ta biyo bayan ruwan sama mai karfin gaske, tare da rusa gidajen jama’a, barnata gonaki, hanyoyi da makamantan su a kananan hukumomi 7- Rafi, Kontagora, Labun, Wushishi, Mashegu, Magama da Gbako da ke jihar.
Ambaliyar Ta Shafi Mutum 239 A Yankin Kontagora Gadar Bida Zuwa Minna Ta Rushe
An bayyana cewar a kalla mutum dari biyu da talatin da tara barnar ambaliyar ruwan sama ya shafa, yayin da mutane biyu suka rasa rayukan su a karamar hukumar Kontagora.
Shugaban karamar hukumar, Hon. Shehu Sarkin Pawa ya bayyana hakan lokacin da gwamnan Neja ya ziyarci karamar hukumar dan jajanta ma wadanda abin ya shafa a garin.
Ambaliyar ruwan saman ya shafi unguwanni shida a cikin garin Kontagora, gwamnan ya ziyarci hayin Hakimi daya daga cikin unguwannin da ambaliyar barnar ruwan ya fi yi wa illa.
Gwamna Sani Bello ya tausaya gami da jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu da mutanen da suka yi hasarar dukiyoyin su sakamakon ambaliyar.
Gwamnan ya umurci ma’aikatar kula da muhalli ta jiha da ma’aikatun da abin ya shafa da su yi hadin guiwa da karamar hukumar Kontagora da su rusa gine-ginen da aka yi akan hanyar ruwa dan kaucewa faruwar lamarin a gaba.
A cewarsa, akwai bukatar mu samar da hanyar ruwa, domin idan ya kawo ruwa su samu hanyar wucewa.
“Mafi yawan gidajen da yankunan nan mun biya su diyya domin su bar wajen amma sun ki tashi. Saboda haka za mu cigaba da aiki kuma za mu rushe gidajen dan samar da hanyar ruwa”, a cewarsa.
Gwamnan ya shawarci jama’a da su cigaba da kare yankunan su domin ruwan sama zai cigaba da sauka.
Kwamishinan ma’aikatar muhalli, Daniel Habila Galadima ya kara da cewar ma’aikatarsa da ma’aikatar albarkatun ruwa, da ta ayyuka da ita kan ta karamar hukumar Kontagora, da masarautar Kontagora zasu yi hadin guiwa dan tabbatar sun bi umurnin gwamnan na yi rushe rushen gidajen da aka gina akan hanyar ruwa.
Kwamishinan ya bada tabbacin samar da tsarin da zai samar da mafita na kaucewa ambaliyar wanda za a samar da shi cikin wannan watan satumbar, tare da yekuwar wayar da kan jama’a illar yin gine gine akan hanyar ruwa.
“A lokacin da muka samar da maslaha ga matsalar magudanan ruwan, akwai bukatar wayar da kan jama’a na kaucewa yin gini akan hanyar ruwa domin samarwa ruwa hanyar wucewa domin kiyaye hanyoyin da ruwa ke wucewa a lokacin ruwan sama”, a cewarsa.
Gwamnan ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Sudan na Kontagora, inda ya bada tallafin kayan abinci da sauran kayan bukatun gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Mutum 300 A 2022 -NEMA
Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa (NEMA) ta bayyana cewa, fiye mutum 300 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a sassan Nijeriya a cikin wannan shekarar.
Shugaban hukumar, Mustapha Ahmed, ya sanar da haka a taron masu ruwa da tsaki a kan hanyoyin rage matsalolin da annoba ke haifarwa, wanda da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar kasar nan.
Ya kara da cewa, suna karbar bayani na neman dauki har sau 50 a kullum, kuma ambaliyar ta shafi fiye da kauyuka 100.
Ya ce, a kullum alkalumman sai kara karuwa suke yi, yana mai cewa, asarar da aka tafka a wannan shekarar har ya fi na ambaliyar da aka fuskanta a shekarar 2012.
A 2012, NEMA ta bayar da rahoton mutuwar akalla mutum 363 inda kuma mutum miliyan 2.1 suka rabu da muhallin su saboda ambaliyar.
Shugaban na NEMA ya zargi gwamnatocin jihohi a kan yadda suka ki amfani da gargadin da hukumar ta bayar wanda hakan ya sanya aka samu matsaloli wajen kai dauki da kuma ceto al’umma da ambaliyar ta shafa.