Bisa ga mayar da hankalin da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Godwin Emefele ya yi a karkashin shugabancin bankin, ta hanyar kirkiro da tsare-tsare, musamman don ya karfafa wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i (SMEs) a daukacin fadin kasar nan, ganin cewa fannin na (SMEs) na bayar da gagarumar gudunmawa wajen taimakawa da kara bunkasa tattalin arziki, bankin ya kirkiro da tsarin zuba kudade ga fannin kanana da matsakaitan sana’o’i.
Har ila yau, CBN a bisa duba na musamman a fannonin bayanai da sadarwa ta kimiyya (ICT), CBN ya kara bunkasa fannin don ya tafi kafada da kafa da na fadin duniya, musamman don a kara karfafa yin kere-kere da kara wa matasa kwarin gwiwar rungumar koyon sana’o’i.
Ganin cewa, Babban Bankin Nijeriya CBN na tafiya ne da zamani ya kuma yi amfani da fasahar zamani da ya kirkiro domin ganin ya habaka fannin na kanana da matsakaitan sana’oi SMEs.
Hatta a daukacin fadin duniya, kasashen da suka ci gaba irin wannan tsarin ne suka runguma domin su kara bunkasa tattalin arzikinsu.
CBN a karkashin wannan shirin samar da daukin kudade a fannin na kanana da matsakaitan sana’oi, ya yi namiji kokarin wajen samar da daukin kudade ga SMEs, musamman domin a kara bunkasa fannin don a kara habaka tattalin arzikin Nijeriya, musamman fannin aikin noma da kere-kere.
Alal misali, a bangaren fannin aikin noma, Emefele ya mayar da hankali a kanan da matsakaitan sana’oi ta hanyar shirin aikin noma na na ba da rance ‘Anchor Borrowers’ inda wannna shirin ya kutsa cikin daukacin fannonin aikin noma na kasar nan.
Har ila yau CBN ya samar da damarmaki ga wadanda za su amfana, CBN ya zuba a kai dauki kai tsaye don a karfafa kanana da matsakaitan sana’oi a cikin sauran shirye-shiye kamar na, bunkasa sana’oi (MSMEDF), wanda zai mayar da hankali wajen tallafa wa sana’oin matasa (YEDP); da habaka shirin zuba jari don yin noma samun riba (AGSMEIS); da shirin samar da kudade ga masana’antu (CIFI); da shirin samar da rance na (CIFI); a cikin shirin Gidauniyar zuba jari na don a karfafa zuba jari na matasa (NYIF).
A karkashin shirin na (NYIF), CBN ya zuba Naira biliyan 75, inda manufar ita ce don a samar da ayyukan yi a tsakanin matasa domin rage radadin talauci da samar da ayyukan da za su kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Bugu da kari, a cikin shirin na (NYIF), kudaden za CBN ya aminta a zuba sun kai daga Naira 250, 000 zuwa Naira miliyan 50, 000,000 CBN zai awaitar da hakan ne a tsawon shekaru uku wanda kuma babu kudin ruwa, inda duk CBN ya yi wannan ne, don kar matasa su zama masu dogaro da kansu, ba tare da jiran aikin gwamnati ba.
A zangon farko na 2022, wadanda suka amfana a fadin kasar nan sun kai 447,671, inda aka samar kasuwancin da yawansa ya kai 58,229, da kuma sauran kasuwancin da suka kai 389,442 da annobar Korona ta shafa.
Har ila yau, a bangaren MSMEDF da CBN ya samar da kudade ga ayyuka 488 a shirin MSME da ake gudanar wa daukacin fadin kasar nan inda wadannan ayyukan suka karade ayyuka guda 12 da ake yi a jihohi da kuma a fannin masana’antu masu zaman kansu dake, da fannin aikin noma, fannin kere-kere, fannin aikin noma, samar da makamashin hasken wutar lantarki da kuma hada – Gadar kasuwanci guda 216,706 tare da samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba a daukacin fadin kasar nan.
Hakazalika, akwai kuma ayyukan na kasauwanci 55,422 wanda aka gudanar wa a karkashin shirin bunkasa Cibiyoyin kasuwanci (EDC) wanda shi ma an samar da dauki.
Wasu alkaluman sun nuna cewa, baya ga fannin aikin noma don samun riba 28,961 da kuma sauran ayyuka da CBN ya zuba kudade a cikin su yake kuma gudanar wa a daukacin fadin kasar nan, CBN ya kuma samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba guda 107,932.
CBN ya yi wannan ne, karkashin shirin kanana da matsakaitan sana’oi na zuba jari wato (AgSMEIS), sannan CBN ya zuba kudade a cikin ayyukan horar da matasa sana’oin guda 395.
Sana’oin da za su amfana su ne, aikin noma, masana’antu, samar da makamashin wutar lantarki, kimiyya da sauransu.
Biyo bayan raguwar da aka samu na samar wa da Gwamnatin Tarayya da kudaden shiga, Babban Bankin Nijeriya CBN ya samar da kudade a cikin tsare-tsare da ke da bukatar a zuba kudaden ba kuma tare da, an ci karo da wata tangarda ba.
Gilbert sanannen mai fashin baki ne a fannin tattalin arziki kuma mazauni a Babbn Birnin Tarayyar Abuja.