Jami’an Hisbah a Jihar Zamfara sun kama wasu mutum biyu mace da namiji suna lalata a bainar Jama’a a wata tashar mota a birnin Gusau ta Jihar Zamfara.
Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun yi lalatar ne tsirara ba tare da la’akari da wani na kallonsu ba.
Hakan tasa jama’ar da ke tashar motar suka kai wa jami’an Hisbah rahoto, Jami’an cikin gaggawa suka isa tashar suka yi awon gaba da su.
Wadanda suka shaida lamarin, sun ce lamarin ya faru ne bayan namijin ya kalubalanci matar kan cewa ya fi ta rashin kunya, inda ita ma ta kalubalance shi, wanda daga nan suka soma wannan aika-aika.
Acewar shaidun, sun ce, lamarin ya faru ne bayan jayayyar Wanda yafi fitsarewa tsakanin namijin da macen, ya kalubalance ta da cewa “in ta isa, ta cire kayanta a tsakiyar Kasuwar, sannan ita ma ta kalubalance shi da hakan, daga bisani kuma suka fara lalatar a bainar Jama’a”
Tuni dai aka gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Kankuri da ke garin Gusau.