• Leadership Hausa
Friday, June 2, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Soke Takarar Dare A Matsayin Wanda Zai Yi Wa PDP Takarar Gwamna A Zamfara

by Sadiq
9 months ago
in Manyan Labarai, Siyasa
0
Kotu Ta Soke Takarar Dare A Matsayin Wanda Zai Yi Wa PDP Takarar Gwamna A Zamfara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wata babbar kotun tarayya a Jihar Zamfara ta soke zaben fidda-gwanin da ya tsayar da Alhaji Dauda Lawal Dare a matsayin dan takarar gwamnan Jihar a PDP a zaben 2023.

Wani tsohon dan majalisar tarayya, wanda kuma ya tsaya takara a zaben, Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya garzaya kotu yana neman a soke zaben fidda-gwani na jam’iyyar PDP da Dare ya lashe, saboda rashin bin ka’ida.

  • Matar Da Ta Sheka Wa Matashi Tafasasshen Ruwan Shayi Ta Shiga Hannun ‘Yansanda A Kano
  • Tagomashin Da CBN Ya Samar Wajen Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i

Da yake yanke hukuncin a ranar Juma’a, mai shari’a Aminu Baffa Aliyu, ya ce kotun ta amince da dukkanin bayanan da mai kara ya yi.

Hukuncin yana kunshe ne a cikin takarda mai shafi 109.

Mai shari’a Aminu ya bayar da umarnin cewa dole ne a sake gudanar da sabon zaben fidda-gwani domin tabbatar da adalci da adalci ga kowane bangare.

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa

Da yake jawabi jim kadan bayan yanke hukuncin, lauyan wanda ya shigar da kara, Barista Ibrahim Ali, ya ce, “Kotu ta duba ingancin lamarin kuma ta yanke hukunci a kan wadanda suka shigar da kara.”

Ya kara da cewa, “Addu’armu ita ce, kotu ta soke zaben fidda-gwani da kwamitin da Adamu Maina Waziri ya jagoranta, sannan kotu ta ba da umarnin a gudanar da sabon zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin PDP da ka’idojinsa suka tanada.

“An yi la’akari da hukuncin da kyau saboda mun tabbatar da shari’armu ba tare da shakka ba kuma mun yi farin ciki da hukuncin da kotu ta yanke.”

Sai dai mashawarcin jam’iyyar PDP a Jihar a fannin shari’a, Barista Bashir Abubakar Masama, ya ce jam’iyyar za ta yi nazari kan hukuncin da za ta dauka, inda ya ce za a daukaka kara kan hukuncin.

Tags: DareHukunciKaraKotuPDPSiyasaTakarar Gwamna
ShareTweetSendShare
Previous Post

Manoma Sun Rungumi Shuka Farin Wake Da Auduga Ta Fasahar Zamani

Next Post

Zulum Ya Bai Wa Matasan Biu 1,000 Tallafin Miliyan 100 Don Yin Jari

Related

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur
Manyan Labarai

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

28 mins ago
Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa

2 hours ago
Tinubu Ya Nada Dele Alake A Matsayin Mai Magana Da Yawunsa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Shiga Wata Ganawa Da Gwamnonin Jam’iyyar APC A Abuja

4 hours ago
Maganar Gwamnan Zamfara Dauda Ya Mallaki Tiriliyan 9 Ba Gaskiya Ba Ne Bata Da Tushe
Siyasa

Maganar Gwamnan Zamfara Dauda Ya Mallaki Tiriliyan 9 Ba Gaskiya Ba Ne Bata Da Tushe

6 hours ago
Cire Tallafin Man Fetur Ba Nan Take Zai Fara Aiki Ba, Sai Karshen Watan Yuni – Tinubu 
Manyan Labarai

Shugaban Nijeriya Na 16: Jan Aikin Da Ke Gaban Jagaban

9 hours ago
Majalisar Dokokin Filato Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansiloli
Manyan Labarai

Majalisar Dokokin Filato Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansiloli

1 day ago
Next Post
Zulum Ya Bai Wa Matasan Biu 1,000 Tallafin Miliyan 100 Don Yin Jari

Zulum Ya Bai Wa Matasan Biu 1,000 Tallafin Miliyan 100 Don Yin Jari

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

June 2, 2023
Takaddama Kan Shirin Daukar Sabbin ‘Yansanda

Yadda Matashi Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 10 Fyade A Bauchi

June 2, 2023
Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa

Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa

June 2, 2023
Yadda Mohammed Bello Koko Ya Tsaftace Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya

Yadda Mohammed Bello Koko Ya Tsaftace Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya

June 2, 2023
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

June 2, 2023
Tinubu Ya Nada Dele Alake A Matsayin Mai Magana Da Yawunsa

Tinubu Ya Shiga Wata Ganawa Da Gwamnonin Jam’iyyar APC A Abuja

June 2, 2023
Wani Soja Ya Hallaka Kwamandansa Ya Kuma Bindige Kansa Da Wasu Sojoji 2 A Sokoto

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3, Sun Kwato Makamai A Kaduna

June 2, 2023
Maganar Gwamnan Zamfara Dauda Ya Mallaki Tiriliyan 9 Ba Gaskiya Ba Ne Bata Da Tushe

Maganar Gwamnan Zamfara Dauda Ya Mallaki Tiriliyan 9 Ba Gaskiya Ba Ne Bata Da Tushe

June 2, 2023
Nijeriya

Samar Da Kyakkyawar Makoma Ga Yaran Nijeriya

June 2, 2023
Shettima

Dole Mu Yi Gaggawar Cire Tallafin Mai Ko Ya Halaka ‘Yan Nijeriya – Shettima

June 2, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.