A yau Litinin, daruruwan ‘Ya’yan kungiyar daliban Jami’o’i ta kasa (NANS) suka datse hanyar zuwa filin tashi da saukar Jiragen Sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed dake jihar Legas.
Daruruwan Daliban sun dauki wannan matakin ne kan cigaba da yajin aikin da kungiyar malaman Jami’o’in kasar nan ASSU ke yi, inda yajin aikin ya janyo dakatar da gudanar da al’amura a Jami’oin Nijeriya.
Kungiyar Daliban wacce ta datse hanyar duk da ruwan sama kamar da bakin Kwarya da ake kwarara wa, sun janyo cunkoson ga ababen hawa da suka biyo hanyar, inda fasinjojin suka tsaya churko-churko.
Bayan Jami’in tsaro sun dakatar da daliban daga shiga tashar Jirgin saman, sai suka datse hanyar zuwa filin jirgin.
Masu zanga-zangar an ruwaito cewa, shugabanin kungiyar ne suka jagoranci zanga-zangar.
Sun bukaci ASUU da ta gaggauta janye wa daga yajin aikin wanda ya shiga cikin wata na bakwai, inda kuma suka nemi Gwamnatin Tarayya da ta biya bukatun Malaman don Daliban su koma azuzuwan su don ci gaba da karatu.