ABDULLAHI KABIR da aka fi sani da Abdul Dan Hausa, mawaki, jarumi kuma mai ba da umarni a masa’antar Kannywood, ya ja hankalin gwamnati kan ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta haramta yin fina-finan da suke nuna ta’addaci. Dan Hausa ya yi wannan kira ne a cikin hirarsu da wakilinmu RABIU ALI INDABAWA, ga yadda hirar ta kasance.
Da farko za mu so ka bayyana wa masu karatu sunanka da tarihinka a takaice
Sunana Abdullahi Kabir, amma an fi sanina da Abdul Dan Hausa, mawaki, jarumi, kuma marubuci na fina-finan Hausa. An haife ni a garin Jere dake Jihar Kaduna, kuma na yi karatuna a garin Jere Firamare da Sakandire, sannan na garzaya Makarantar Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Zariya, wato Federal College Of Education Zariya, na yi karatun NCE dina, daga nan kuma ban ci gaba ba.
To kana da wata sana’a bayan harkar fim?
Da farko dai ina sana’ar dinki, kuma ina sana’ar waka da kuma ba da umarnin fina-finai
To me ya ja hankalinka zuwa harkar fim bayan kana da sana’a?
Eh to gaskiya kamar yadda kai bayani, na fi karfi a harkar waka saboda abin da ya fara jawo ni kenan harkar fina-finai da sauransu. Abin da ya jawo shiga Kannywood musamman bangaren waka, gaskiya waka yadda na dauke ta hanya ce ta isar da sako cikin sauki, wanda a lokaci daya za ta iya zagaya duniya ma gaba daya saboda irin wasu abubuwa da ake yi masara kyau, da kuma nishadanyat da mutane, da sauran wasu abubuwa za ka iya fadakarwa kan irin abubuwan da basu dace ba.
Ya zuwa yandu ka kai kamar shekara nawa kana waka?
Na kai kamar shekara 15 zuwa 20, saboda ina ganin tun 2009 na fara harkar waka
Yawan wakokinka za su kai kamar nawa?
Wakokina za su kai kamar guda 30
A cikin wakokinka, wacce da wacce ce su ka yi fice?
Eh to wakokin suna da yawa, akwai wadda na yi ta akan zaman lafiya da Gwamnan Jihar Neja ya sa gasa Abulolo, wanda kuma a mawakan Hausa ni na zo na daya a wannan gasa, akwai wakoki kuma na soyayya da sauransu.
A cikin fina-finan Kannywood, wane fim ne aka yi amfani da wakarka da idan aka ji za a gane ta, ko kowa dai wakokin siyasa kake yi da na biki?
Eh to gaskiya a wannan lokacin babu wani fim da aka yi amfani da wakata, amma dai akwai kundi da ake fitarwa wadda ko ba ni zan hau ta ba, domin akwai wasu idan za su yi bidiyo sai dauka su yi amfani da ita.
To tun da maganar Kannywood muke, ka taba fitowa a wani fim na barkwanci ko ba na barkwanci ba, ko kuma mai dogon zango da ake yi yanzu?
Eh, akwai wani fim da na fito a ciki wanda a yanzu haka ma ana ci gaba da aikin fim din, shima mai dogon zango ne mai suna MARWAN. Sannan kuma kwai fina-finai da dama da na dan taka rawa a cikinsu.
Yanzu mene ne burinka a rayuwa?
Buri na a rayuwa, ina so na ga cewa nima na shahara kamar yadda sauran mawaka da jarumai suka shahara a duniya haka nake so na kasance a cikinsu. To amma galibi wasu abubuwa idan baka da hanya ko ba ka da kudi, wasu kalubale ne da mutum yake fuskanta a irin wadannan abubuwan.
Ka san idan mutum ya shigo tsangayar Kannywood, abin da wasu suke ganin ya kan daukaka mutum shi ne ubangida, kai waye ubangidanka a wannan tsangaya, kamar wanda ya yi maka hanya ka shigo ko wani kamfani da ya tsaya maka?
Akwai wani Darakta ana kiransa Dan’azumi Baba, shi ya yi min hanya na shigo wannan masa’anta ta Kannywood. To amma duk da yanayin abubuwa yanzun nan gaskiya shi kansa bai cika yin ayyuka sosai ba, saboda za ka ga galibi Daraktoci, da Furodusoshi su kan duba sababbin fuskoki ne da kuma wanda zai iya kawo musu abin da suke so, musamman za ka ga wasu jaruman yanzu suna amfani da kudinsu ne domin a sa su a fim da sauran wasu abubuwa.
Ka ja hankalin gwamnatin akan yakamata ta dakatar da finanan da ake shirya su akan abin da ya shafi ta’addanci, me ka hang aka yi wannan kira?
Eh to na yi wannan kira ne saboda za ka ga galibi mutanenmu ta nan ne suke koyon wasu abubuwa da suka shafi ta’addanci. Misali yanzu idan ka kalli fina-finan da ake yi da suka shahara, za ka ga akwai abubuwa na ta’addanci a cikin wadannan fina-finan, shi ya sa nake kokarin nusar da gwamnati akan yakamata ta tadakatar da duk irin wadannan fina-finan da ake kokarin fita da ta’addanci a fili domin taimaka wa harkar tsaro.
Wane ne babban abokinka a tsangayar Kannywood?
Akwai abokina ana kiransa Aliyu Karaye, da kuma Adam Dan Jalaika, wadannan su ne abokaina da muke wannan gwagwarmaya da su a yanzun nan.
Daga lokacin da ka shiga Kannywood zuwa yanzu wadanna nasarori ka samu?
Na samu nasarori, domin a kan gayyace ni na yi wakar aure, ko wakar bikin cikar shekarar wani, da sauran wasu abubuwa da suka shafi harkar waka. Sannan kuma a shigowata din nan ce har na fara ba da umarni a wasu fian-finai wanda kuma hakan ne ake dauka na na ba da umarni a wasu fina-finai, sannan kuma karin dadawa kamar yadda na yi maka bayani, a waccan wakar da na yi wa shi Mai Girma Gwamnan Jihar Neja da Allah ya bani sa’a na zo na daya na samu kyaututtuka da yawa, wanda har a lokacin ma an so a dauki nauyinmu zuwa kasar waje domon gabatar da wasu shirye-shirye Allah bai kaddara ba, amma a wancan lokacin har alawus ake bamu duk wata, ka ga hakan babbar nasara ce da ba zan taba mantawa da ita ba.
To idan samu nasarori a kan samu kalubale a rayuwa, da shigarka Kannywood wane kalubale ka fuskanta?
Kalubalen da fuskanta, tun a lokacin da na ambata zan shiga sai ka ji mutane na cewa za su hada ka da wane da wane, sai daga baya gane basu da wata hanya akan hada ka da wanda suke fada, yana daga cikin abin da ya sa ma na saki layin duk wani wanda zai min, in dai ba na ga zahiri za ka yi min hanya bane a kan hakan. Sannan akwai matsaloli na rashin kudi musamman a lokacin da waka za ta karbe ni kuma na ga hanyar isar da sako, a lokacin in ba kana dan abin da za ka je wurin buga waka ba sai dai ka hakura, ka ga wannan shima kalubale ne a wannan harka.
To wace shawara za ka bai wa wadanda suke kokarin shigowa Kannywood da kuma na ciki?
Shawarar da zan ba wa wadanda suke kokarin shiga wannan masa’anta, sai sun yi hakuri da wasu abubuwa da su ne za su kai su ga nasara. sharafi na Allah ne, ba lallai ne ka ce a lokacin da ka shiga kuma a wannan lokacin kake so ka daukaka ko kuma lokacin ne kake so a haska ka ba, wani ya yi bauta sannan ka ga an fara s aka a fina-finai da sauransu.
Su kuma wadanda suke cikin wannan wuri ya kamata su gane cewa in yau su ne gobe ba su bane, dole ne su koya wa wadanda suke son shigowa wannan masa’anta yadda za su rika tafiyar da al’amuransu wanda idan gobe babu su to za a yi alfahari da su, kuma suma za su yi alfahari da su, domin a haka ne ake samun wadanda za su maye guraben wasu yayin da babu wasun.
Wane kira za ka yi ga wasu matan da za su shigo Kannywood bayan sun shahara a masa’antar daga baya sai su koma Soshiyal midiya suna abubuwan da basu dace ba kamar su bayyana tsiraici da kalamai marasa amfani?
Irin wadannan mata, da farko dai zan ce su ji tsoron Allah, domin kamar yadda aka ce wasan kwaikwaiyo, to fa al’umma na kwaikwayonsu ne a cikin fim ko kuma a wajen fim. Domin irin abubuwan da wadannan ke yi za ka ga ya saba wa addini, al’ada da kuma dabi’u masu kyau na Malama Bahaushe. Musamman Furodusoshi da Daraktoci ya kamata su ankare kan irin wadannan abubuwa da mata suke yi domin hakan zai zubar musu da kima da mutunci a idon al’umma.
Mun gode
Ni ma na gode