Fitacciyar Jarumar da ke haskawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, DIAMOND ZARAH Ta bayyana cewa ta shiga masana’antar shirya fina-finan Hausa ta kannywood ne bisa kaddarawar haka da Allah ya yi mata, shi ya sa da za a tambaye ta shekara 10 baya ko za ta yi fim a gaba ba za ta taba yarda ba.
Akwai ma wasu batutuwan, ga dai tattaunawar kashi na farko tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki
Sunana Zarah Mohammad, wadda aka fi sani da Diamond Zarah.
Me ya sa ake kiranki da Diamond Zarah?
Eh! toh lakani ne kawai.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Kamar yadda na fada a baya, sunana Zarah Mohammad. An haife ni a kasar Nijar nayi karatuna a can, na tsaya a matakin sakandare, ba ni da aure, sannan ina zaune a garin Kano, na fara fim tun 2018 karkashin jagorancin iyayen gidana kamar; Awwal D. Yakasai, Mai Shabbabu da kuma Ali Gumzak.
Toh ya batun shekaru?
Shekaruna 24. An haife ni 25 ga watan March shekara ta 1998.
Wace rawa kike takawa a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood?
Jaruma ce ni a masana’antar kannywood kuma mai tallace-tallace.
Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar?
Abin da ya ja hankalina ba komai ba ne face na ce kaddara, Bayanin kenan ‘Because’ cewar; ina so tun ina karama ‘this and that’ duk fada kawai ake yi ‘sometimes’ dan ni idan aka ce min zan yi fim shekara goma baya ba zan taba yarda ba, So kaddara ta ce ta kawo ni fim, mai kyau ce ko mara kyau sani sai Rabbi.
Za ki yi kamar shekara nawa yanzu cikin masana’antar?
Zan yi kamar shekara hudu zuwa biyar cikin masana’antar.
Tsakanin fim da tallace-tallace wanne kika fara?
Na fara da fim daga baya na fara tallace-tallace.
Da wanne fim kika fara?
Na fara da fim din Zuma da Madaci, har yanzu ba a fitar da shi ba, Ni ce na ja fim din da ‘support’ din Adam A. Zango, Ali Nuhu, Abdul M. Shareef, Halima Atete da sauransu.
Fim din yana kan hanyar fita ne ko kuwa an ajjiye shi gefe guda ne, kuma me dogon zango ne (Series) ko kuwa takaitacce ne?
‘Da’ aka yi shi, fim ne takaitace, amma yanzu za a maida shi mai dogon zango ‘soon’ in sha Allah, na yi nasara jan ragamar fim din a dalilin tantacewa da ake yi na jarumai domin samun abin da ake so.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Gaskiya Alhmdulillah ban ga wata gwagwarmayar a zo a gani ba, sai ‘yan abubuwa da ba za a rasa ba, wanan kuma ‘for me’ abu ne da kowacce sana’a ta gada ne.
Zamu ci gaba wani lokacin