Hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) reshen Jihar Bayelsa ta gudanar da taron ganawa da masu ruwa da tsaki da shugabannin al’ummar Nijar, Benin, Togo, Ghana da kuma na Mali a Yenagoa.
Hukumar NIS reshen Jihar Bayelsa ta bayyana taron ganawar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 29 ga watan Satumbar 2022.
A zaman ganawarsa na musamman da kwanturololin hukumar na faɗin ƙasar nan a shalkwatan hukumar da ke Abuja, Shugaban hukumar NIS, CGI Isah Jere Idris ya ba su umurnin sa ido da duba waɗanda ba ‘yan Nijeriya ba domin shirin tunkarar zaɓen 2023, a cikin umurnin har da hana baƙin-haure yin zaɓe ko mallakar katin zaɓe ko kuma dukkan kayayyakin da ke da alaƙa da zane domin tsare iyakokin ƙasar nan.
Domin ƙarin haske a kan wannan umurni, hukumar NIS reshin Jihar Bayelsa ta yi gaban kanta wajen sake ilmantarwa da wayar da kan bakin-haure da ke zaune a Jihar Bayelsa domin cika wannan umurni wajen saka ido da kulawa da kwararowar baƙin-haure a cikin jihar, inda ake binciken maɓoyansu da ke saƙo da lungu a Yenagoa.
Sanarwar ta nuna cewa wasu daga cikin baƙin-hauren suna gudanar da sana’o’in da suka haɗa da gadi, wankin takalma, tala, sayar da fiyowata da yin acaɓa a ciki da wajen garin Yenagoa.
Dukkan ɗaukacin rassan hukumar NIS an ba su umurnin sa ido da kulawa wajen bayyana wa hukumar rahoton sirri kan ayyukan da baƙin-haure suke gudanarwa a ƙananan hukumomi guda 8 da ke faɗin Jihar Bayelsa baya ga babban birnin jihar Yenago, wannan ƙoƙari ne na faɗaɗa umurnin da shugaban hukumar NIS ya bayar na ganin ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, a matsayinsa na shugaban hukumar da ke kulawa da iyakokin Nijeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan tsare-tsare zai ci gaba da gudana har zuwa zaɓen 2023 da ake fuskanta da kuma bayan zaɓen.