Mai yiwuwa wannan shi ne gidan tarihi da ba a saba ganin irinsa ba a duniya, wanda aka cika shi da kayan tarihi da suka sauya duniya. Sai dai ba a barin al’umma su shiga cikin gidan.
A nan wurin ne kawai masu ziyara za su ga bindigar da aka samu a wajen Osama bin Laden lokacin da aka kashe shi, kusa da wata rigar fata ta Saddam Hussein.
- Kiraye-Kirayen Neman Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Wasu Filayen Jiragen Sama Na Jihohi
- Cikar Nijeriya Shekara 62 Da ‘Yancin Kai
Barkanmu da zuwa gidan tarihin sirri na CIA.
A cikin ginin shelkwatar hukumar leken asiri ta Amurka yake a Langley birginia.
An sake yi wa gidan kwaskwarima a wani bangare na cikar shelkwatar shekara 75 da kafuwa.
An bai wa wasu ‘yan jarida kalilan damar shiga wurin ciki har da BBC, amma fa duka da jami’an tsaro ciki da waje da suka yi musu rakiya.
Cikin kayan tarihi 600 da ake da su akwai sauran kayan aikin da ‘yan leken asiri suka yi amfani da su a yakin cacarbaka – akwai wani bera da ake aika shi da sako a boye, akwai wata kyamara a jikin taba sigari da ake amfani da ita, ga wata tattabara da kyamarar leken asirin da aka makala a jikinta.
Akwai kuma bayanai kan wasu ayyukan hukumar CIA da suka gabata da kuma na yanzu da ake yi.
Akwai kuma hoton wani gini wanda aka gano Osama bin Laden a cikinsa a Pakistan.
An nuna wa Shugaba Obama hoton ginin kafin ya amince a kai harin da ya yi sanadin mutuwar shugaban na kungiyar al-kaeda a 2011.
“Samun damar ganin abubuwa a jikin hoton fasahar tiridi (3D) yana taimakawa masu tsara dokoki… da kuma su kansu kan yadda za su tsara ayyukansu,” kamar yadda Robert Z byer Daraktan gidan da ya zagaya da su ya shaida musu.
A ranar 30 ga watan Yulin wannan shekarar wani harin makami mai linzami ya kara dira cikin wani gida, amma a wannan karon ya samu sabon shugaban kungiyar al-kaeda ne Ayman Zawahiri.
Harin ya samu Zawahiri ne cikin wata baranda, bayan jami’an hukumar leken asiri ta Amurka sun kwashe watanni suna nazartar abubuwan da yake yi.
“Harin ya nuna karara yadda jami’an yaki da ta’addanci suka fahimci rayuwar Zawahiri,” in ji Mista Byer.
An tsara bangaren farko na gidan tarihin ne daga abubuwan da suka soma faruwa – kamar kafa ita hukumar a 1974 zuwa yakin cacar-baka, zuwa harin 11 ga watan Satumbar 2001, har da makaman da ‘yan uwan wadanda aka kashe suka kawo a matsayin gudunmawa.
Wadanda suke sauraren bayanin jami’an hukumar CIA ne da kuma jami’an da suka zo ziyarar.
Bayanan ba su takaita ba kawai a kan nasarori ba, a’a akwai bangaren da yake magana a kan harin da CIA ta kai domin kifar da gwamnatin Fidel Castro a Cuba wanda bai yi nasara ba, akwai kuma hujjoji da gazawar da suka yi na nemo makaman kare-dangi a Iraki.
“Wannan ba za mu kira shi gidan tarihi ba kawai. Akwai bangaren ayyuka da muke nuna wa jami’an CIA, domin bankado tarihinmu masu kyau da marasa kyau,” in ji Mista Byer.
“Muna tabbatar da cewa jami’anmu sun fahimci tarihinsu, domin su yi ayyuka masu kyau nan gaba. Za mu dauki darasi daga nasarorinmu, da kuma gazawarmu domin a gaba mu gyara.”
Wasu daga cikin ayyukan CIA da ba a fiya ji ba ko gani – kamar su aikin hadin gwiwa da M16 domin kifar da gwamnatin dimokuradiyya da aka zaba a Iran da kuma na baya-bayan nan wanda ya hada da azabtar da mutanen da ake zargi da hannu cikin harin ta’addancin 2001.
‘Ba za mu iya tabbatarwa ba ko mu musanta’
bangare na biyu na gidan tarihin ya mayar da hankali kan wasu ayyuka na musamman.
Kalmar da muke cewa ‘Ba za mu iya tabbatarwa ba ko kuma mu musanta’ kalma ce da wadanda suke tattarowa hukumar leken asirin bayanai, kuma an samo asalinta ne daga wani tarihi a cikin gidan wanda ake amfani da shi da ba a taba gani ba kafin yanzu.
A karshen shekarun 1960, wani jirgin ruwan Tarayyar Sobiyet ya bata a wani wuri a teku. Bayan Amurka ta gano inda yake, CIA ta yi aiki da wasu manya-manyan kayayyakin fasaha domin gano tarkacensa da kuma fasahar da aka tattara cikinsa.
Gidan tarihin yana kunshe da samfur na jirgin karkashin teku na Tarayyar Sobiyet da kuma tufafi, da kuma tire na ajiye guntayen taba.
Akwai wani gashin doki da mataimakin daraktan CIA ya sanya domin yin bad-dasawu yayin da ya kai ziyara wurin da jirgin yake. Nasarar da aka samu a wannan aikin ba ta da yawa saboda jirgin ya karye ko da yake an samu wasu sassansa.
“Galibin abubuwan da aka samo a cikin jirgin karkashin tekun har yanzu ba a bayyana su ba,” a cewar Mista Byer.
Lokacin da labari ya fita game abin da ake kira Project Azorian kafin a fitar da sauran sojojin ruwa, an shaida wa jami’ai su bayyana cewa ba “za su iya tabbatarwa ko musanta” abin da ya faru ba – wani zance da a yanzu aka fi sani da “Glomar response” kuma har yanzu ana amfani da shi.
Akwai kuma wasu kayayyaki da aka tsara wasan kwaikwayon bogin nan mai suna Argo. Hakan ya bayar da dama wajen ceto wasu ma’aikatan difilomasiyya da aka tsare a Iran bayan juyin-juya halin 1979, abin da daga bisani aka juya shi zuwa fim din Hollywood.
An baje-kolin wasu kayayyaki da aka tsara wajen yin fim din na bogi wadanda ma’aikatan difilomasiyyar da aka tura can kasar suka yi ikirarin yi.
An tsara zane-zanen kayyakin ne ta yadda da wahala mutum ya fahimci sakon da ke cikinsu.
Kuma da yake muna magana ne a kan fahimtar sakonni, a silin din gidan tarihin akwai wasu sakonni da ke dauke da wasu lambobi masu wahalar fahimta.
Burin jami’an CIA shi ne a rarraba wa jama’a bayanan a shafukan sada zumunta domin ganin ko za su iya fahimtar su.
Kazalika za a wallafa wasu daga cikin bayanan a shafin intanet. Don haka a iya cewa wadannan bayanai su ne mafi girma da mutane suka gani game da hukumar leken asirin.