Wasu wakilai shida na kwamitin zartarwa a jamiyyar PDP, sun zargi shugaban jamiyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, da basu cin hancin miliyoyin naira.
Wakilan wadanda suka fito daga shiyyar kudu, sun shelanta cewa, sun mayar da kudaden cin hancin akalla naira miliyan 28 zuwa 36 ga assun PDP.
- An Nada Sanatan PDP Cikin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu
- Rikicin Cikin Gidan APC Da PDP: Shin ‘Yan Jihar Ribas Kadai Aka Bata Wa Rai?
Wakilan shida sun hada da; Dan Orbih, Mataimakin shugaban PDP na shiyar kudu da Stella Effah- Attoe, shugabar mata ta kasa da Taofeek Arapaja, mataimakin shugaba na kasa reshen kudu, sai Olasoji Adagunodo da mataimakin shugaban na kasa na shiyyar Kudu masu Yamma.
A cikin wata wasika, sun yi zargin cewa, Ayu ya ba su cin hancin ne don su biya kudin haya na shekaru biyu.
Sai dai, a cikin sanarwar da sakataren yada labarai na PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a daren jiya, ya karyata zargin, inda ya ce manufa ce kawai ta son janyo rudani da karkatar da tunanin jama’a.