Kakakin majalisar dokokin Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya bayyana yadda ‘yan ta’addar Darul-Salam suka sa shi kuka.
Abdullahi wanda ke wakiltar mazabar Ugya/Umaisha a jihar ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga wasu al’umma da ambaliyar ruwa ta shafa.
- Wadanne Abubuwa Ne Ake Iya Fasa Aure Saboda Su?
- ‘Yan Kwamitin Zartarwa 6 Na PDP Sun Zargi Ayu Kan Ba Su Cin Hanacin Miliyoyin Naira
Ya ce ayyukan ‘yan ta’addan Darul-salam sun kusan tilastawa mutane daina zirga-zirga a hanyar Toto-Ugya-Umaisha, inda ya ce jama’a sun jajanta bayan shigar gwamnatin jihar.
“A gaskiya mun samu matakin da mutanen da ke tafiya a kan titin Toto-Ugya-Umaisha suka daina bin hanyar saboda harin da ‘yan ta’addar Darul-Salam suka kai musu amma Alhamdulillahi yau an samu wani babban ci gaba ga jama’ata.
“A gaskiya a ranar da na ji cewa ‘yan ta’addar Darul-Salam sun mamaye mazabata, sai dana sauko daga kan gadona na fara kuka.
Daga baya na je na yi alwala na yi sallar nafila raka’a biyu”.
Ya yi kira ga al’ummar mazabarsa da su mara wa gwamnatin APC karkashin jagorancin Abdullahi Sule baya, domin inganta tsaro da rayuka da dukiyoyi a yankin.
Ya kuma bukaci matasa da su ci gaba da zaman lafiya da bin doka da oda ga hukumomin da aka kafa musamman a daidai lokacin da ake gudanar da yakin neman zabe.