Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni yayin da yake amsa tambayoyi a taron manema labaru da aka saba yi a yau Laraba cewa, Xinjiang ita ce cibiyar samar da sinadarin polysilicon mafi muhimmanci a duniya, wanda ake amfani da shi wajen samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana. Kasar Amurka ta kirkira karya da ta kira wai “aikin tilas” a Xinjiang, don cimma mummunan burinta na yin magudin siyasa da nufin lalata fa’idojin takarar masana’antun Xinjiang, da fitar da masana’antar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana daga kasar Sin.
Rahotanni sun nuna ce, wakiliyar kasuwanci ta kasar Amurka Katherine Tai ta bayyana a baya-bayan nan cewa, kashi 85 cikin 100 na bangarorin batir din samar da wutar lantarki bisa hasken rana da ake samarwa, a kasar Sin ake samar da su, kuma wasu masana’antu dake samar da su suna yankin Xinjiang ne, inda ake fama da matsalar da ake kira wai “tilasta yin aiki”.
Game da hakan, kakakin ya jaddada cewa, “Abin da Amurka ta yi zai hana kasuwancin kayayyakin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da ake yi yadda ya kamata, kana zai kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki na yau da kullum, da dakushe kokarin da duniya ke yi na magance sauyin yanayi, wanda a karshe zai kawo koma baya ga ita kanta Amurka da kuma lalata muradunta. Kasar Sin kamar yadda ta saba, za ta dauki dukkan matakan da suka dace, don kiyaye ‘yanci da muradun kamfanoninta.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)