Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, kasar Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire tare da bude kofa ga kasashen ketare.
Alkaluman ci gaban kirkire-kirkire na kasa da kasa na shekarar 2022 da hukumar kare ikon mallakar fasaha ta duniya (WIPO) ta fitar jiya Alhamis, ya nuna cewa, kasar Sin ta zo ta 11 a kididigar kirkire-kirkire ta duniya, karuwar mataki daya kan na shekarar da ta gabata.
Mao ta ce, wannan ya sake tabbatar da manyan nasarorin da kasar ta samu a fannin kare ikon mallakar fasaha. Kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha da cudanya a fannin sadarwar zamani ta duniya, da kare ikon mallakar fasaha yadda ya kamata, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha a dukkan fannoni.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta rungumi hanyar raya ikon mallakar fasaha mai sigar musamman na kasar Sin.(Ibrahim)