Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya misalta jam’iyyar a matsayin jam’iyya mai tasirin da za ta iya lashen 2023 da ke tafe.
Atiku ya bayyana hakan a filin wasanni na Abubakar Tafawa Balewa, a ranar Laraba lokacin da ya karbi sama da mutum 25,000 da suka sauya sheka daga wasu jam’yyun zuwa PDP a Jihar Bauchi, ya misalta hakan a matsayin alamun nasara ga jam’iyyar.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Abuja-Kaduna
- NCCE Ta Garkame Kwalejojin Bogi 41 Da Ke Bayar da Shaidar NCE A Bauchi
“Yau kuma ga abun farin ciki ya same mu mun samu karuwa. Babu wani da zai zo ya yi hamayya da PDP a Bauchi ba wanda zai yi hamayya da Kauran Bauchi.”
Wazirin Adamawa, ya nuna kwarin guiwarsa da cewa dandanzon al’ummar da ya gani a wajen taron hakan ya nuna kyakkyawar alamar nasarar jam’iyyar a yayin zaben mai zuwa.
Daga bisani ya yi amfani da damar wajen jinjina wa kokarin gwamna Bala Muhammad na kyautata jihar tun lokacin da ya zama gwamna zuwa yanzu, “Muna taya ka murna da wannan kyakkyawan ci gaba da aka samu a Jihar Bauchi. Watannin baya da suka wuce na zo na kaddamar da wasu ayyyuka masu dumbin yawa wadanda ban taba gani a Bauchi ba sai a wannan karon a karkashin gwamantin Kauran Bauchi kuma a karkashin jam’iyyar PDP.
“Jama’ar Bauchi muna son mu dauki wannan damar mu taya ku murna domin yanzu kun samu gwamnati ta gari wacce ta ke kawo ci gaba a Jihar Bauchi.
“Amma ya kamata ku yi tunani cewa siyasar arewa daga nan Bauchi ta fara, nan ne cibiyar siyasa ta arewa don haka bai kamata ku rike siyasar PDP da bayan hannu ba.”
A nasa bangaren, gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi kuma dan takarar gwamnan jihar a zaben 2023, ya nuna Atiku a matsayin hazikin da al’ummar Bauchi ke so a kowane lokaci kuma suka amince zai iya kai Nijeriya mataki na gaba.
“Muna tabbatar maka cewa mutanen Bauchi sun dawo suna tare da kai suna sonka kuma suna tare da mu. Muna gode musu saboda suna nuna kauna a gare mu bisa ayyukan da suka ga muna yi sakamakon dama da kuka ba mu. Kuma kai ka yi kokari a rayuwa, ka kasance mai taimakon mutane ka agaza musu.
“Kuma al’ummar Nijeriya sun san cewa idan ka zo, za ka taimaka ka azaga wa kowa.
“Ina tabbatar maka wadanda mutanen da ka gani naka ne. Kuma namu ne,” a cewarsa.
Gwamna Bala ya amshi bakoncin dan takarar shugaban kasa da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyyar PDP na kasa Ayu Iyorchia, tare da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
Shi kuma shugaban jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam, ya shaida cewar sama da mutum dubu ashirin da biyar da suka kunshi tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauchi da tsohon kakakin majalisar jihar ne suka saura sheka zuwa PDP.
Akuyam, ya ce irin dumbin jama’ar da suka fito domin tarbar Atiku da wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar sun yi bisa ganin dumbin ayyukan raya jihar da gwamantin PDP ta gudanar a jihar.
“Wadanda suka dawo wannan jam’iyyar sun dawo ne bisa ganin irin dumbin ayyukan da aka gudanar kuma gani suka yi ana abun kirki ana ayyukan da suka dace a Jihar Bauchi.
“Mutanen da ka karba yau sama da mutum dubu ashirin da biyar a cikinsu akwai tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauchi wanda ya sauka kwanan nan, akwai tsohon Kakakin Majalisa duk ‘yan jam’iyyar APC ne suka dawo cikin PDP.”
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ayu Iyorchia, shi ne ya yi wankan shigo da wadanda suka sauya shekar zuwa PDP a jihar.