Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Dai Bing ya bayyana cewa, ana samun albarkatun halittu masu yawa a nahiyar Afirka, kuma akwai kyakkyawar makoma a wannan fanni, sai dai ya kamata kasa da kasa su taimakawa gwamnatocin kasashen Afirka, wajen inganta karfinsu na amfani da albarkatun halittu, da kuma sa kaimi ga kafa tsarin darajar albarkatun duniya bisa adalci.
Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya, a gun muhawara na kwamitin sulhu na MDD kan batun yaki da kungiyoyin bata gari da ‘yan ta’adda, wadanda suke tattara kudi ta hanyar fasa kaurin albarkatun halittu.
A cewarsa, inganta karfin gwamnati kan aiwatar da harkokinta, zai rage yawan laiffukan fasa kauri.
Ya ce ya kamata kasa da kasa su goyi bayan gwamnatocin kasashen Afirka wajen taka muhimmiyar rawa a fannin amfani da albarkatunsu don inganta karfinsu a fannonin tsara shirye-shiryen raya sana’o’i, da sa ido ga hada-hadar kudi, da aiwatar da ayyuka bisa doka da sauransu, yana mai cewa ta hakan, za a iya amfani da albarkatu wajen samun ci gaba.
Dai Bing ya kara da cewa, samun ci gaba mai dorewa ba tare da la’akari da bambance-bambance ba, shi ne tushen samun zaman lafiya da karko mai dorewa.
Kuma Sin tana fatan kasa da kasa musamman kasashe masu ci gaba za su cika alkawarinsu na kara taimakawa kasashen Afirka wajen kawar da talauci, da tabbatar da wadatar abinci, da gina ayyukan more rayuwa, da sa kaimi ga ba da ilmi da samar da ayyukan yi da sauransu, don ba su gudunmuwa ta hakika wajen samun ci gaba. (Zainab)