• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Abokin Daka Akan Sha Gari

by CMG Hausa
3 years ago
Gari

Kamar yadda muke ji yau da kullum daga bakin masana, cewa babu wata kasa a duniyar nan da za ta samu cikakken ci gaba, ba tare da bunkasa yankunanta na karkara ba, muna iya ganin shaidu na zahiri don gane da hakan a nan kasar Sin.

Mahukuntan kasar Sin sun jima da fahimtar muhimmancin kawar da kangin talauci da raya karkara, a matsayin babban jigon gina kasa, tare da tabbatar da ba a bar wani bangare na alummar Sinawa a baya ba.

Kaza lika da yake yankunan karkara na taka muhimmiyar rawa wajen gina kasa, ta hanyar samar da nauo’in cimaka, kama daga hatsi, da kayan lambu da ’yayan itatuwa, gudummawar sassan na karkara na kan gaba wajen tabbatar da samar da isasshen abinci ga daukacin yankunan kasar, hakan ya sa har kullum, gwamnatin Sin ke kara azama wajen ganin yankunan karkara sun kara azamar fita daga talauci, da samun kyakkyawar rayuwa.

Bahaushe kan ce Da ruwan ciki a kan ja na rijiya, har kullum mahukuntan Sin na dagewa wajen ganin yankunan karkarar kasar sun samu dukkanin tallafin da suke bukata na raya sanao’i, da inganta damammakin samar da ilimi, lafiya da sauran ababen more rayuwa.

Wannan ne ma ya sa duk da yawan ayyukan dake gaban shugaban kasar Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kolin JKS, ya kan ware lokuta musamman domin ziyartar yankunan karkarar kasar Sin, ya gana da jamaar yankunan, ya ji koken su, da yanayin rayuwar su, da irin ci gaban da suka samu karkashin manufofin wanzar da ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

Wani abun birgewa game da manufar gwamnatin Sin mai ci shi ne yadda take karfafa gwiwar yankunan karkara, wajen tashi tsaye domin dogaro da kai. Cikin kalaman shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa Idan har burin mu shi ne kallon na sama da mu, muna neman a taimaka mana, muna korafin rashin samun dama kamar saura, ta yaya za mu iya samun karfin gwiwar yakar fatara?”
Ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kauyen Yongfeng na lardin Sichuan a cikin makon nan, ta shaida wannan muhimmiyar manufa, domin kuwa yayin da yake rangadi a kauyen na Yongfeng, ya nazarci yadda ake kara azamar kyautata samar da kayan noma na zamani, da matakan bunkasa samar da hatsi a yankin, da ayyukan raya karkara, da matakan dakile yaduwar annobar COVID-19.

Wannan ziyara ta shugaba Xi, ta dada shaida burin mahukuntan Sin, na yin tafiyar samar da ci gaba tare da dukkanin yankunan kasar, ta yadda kowa zai ci gajiya daga alfanun manufofin kawar da talauci, da wanzar da ci gaba, da gina alumma mai makomar bai daya ga kowa, kamar dai yadda a kan ce Da abokin daka a kan sha gari. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

October 20, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Next Post
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025
Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

October 20, 2025
Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

October 20, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025
Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.