Beijing, fadar mulkin kasar Sin a ranar 16 ga watan Oktoban da muke ciki, taro mai muhimmanci matuka yayin da al’ummar Sinawa ‘yan kabilu daban-daban suke kokarin gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni, tare kuma da cimma burinsu na kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, da ke bin tsarin demokuradiya, wa yin kai da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
Birnin Shanghai yana kudu maso gabashin kasar Sin ne, kuma a matsayinsa na babban birnin kasa da kasa na zamani wanda ke babban tasiri a fadin duniya.
- Bukatar ‘Yan Siyasa Su San Kalaman Da Za Su Furta Lokacin Kamfen
- Kotu Ta Yanke Wa Wani Tsoho Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Har Abada Kan Laifin Fyade A Jigawa
A gabannin wannan babban taro, mazauna birnin da yawansu ya kai miliyan 25 sun akara nuna kwazo da himma domin ba da gudummowarsu wajen cimma burin tabbatar da ci gaba mai inganci.
Dakin nuna tarihin kera jirgin ruwa na kasar Sin
Kwanan baya an shirya bikin baje koli mai taken babban birnin fasalin kasa da kasa karo na farko a dakin nuna tarihin kera jirgin ruwa na kasar da ke gabar kogin Huangpu da ke birnin Shanghai na kasar.
Kamar yadda aka sani, a watan Disamban bara ne wato shekarar 2021, hedkwatar rukunin kera jiragen ruwa na kasar Sin ta kaura daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai, kawo yanzu alkaluman ma’aunin kera jiragen ruwa na rukunin, na ci gabada zama a sahun gaba a fadin duniya, inda mataimakin babban manajan rukunin Sun Wei ya yi tsokaci da cewa, “Za a tsara shirin raya kasa bisa manyan tsare-tsarea yayin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin dake tafe, a matsayin rukuninmu na zama babban kamfanin da ke karkashin jagorancin kwamitin tsakiyana JKS, za mu kara mai da hankali kan gina dandalolin kirkire-kirkire da suka kunshi cibiyar nazarin babban aikin kera jirgin ruwa a Shanghai, da muhimmin dakin gwajin kimiyya da fasahar tsaron kasa, ta yadda za a gina cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a bangaren kera jirgin ruwan teku a Shanghai.”
Yankin ciniki maras shinge na Lingang
Hakika ban da cibiyar jirga-jirgar kasa da kasa da ake ginawa a Shanghai, akwai sauran manyan ayyuka da ake ginawa a birnin a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.
A watan Nuwamban shekarar 2018, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinpingya sanar yayin bikin kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko cewa, za a bai wa birnin Shanghai sabbin ayyuka gudauku wato kafa sabon yankin ciniki maras shinge, da kafa tsarin hada-hadar kudi kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha tare da kafa tsarin yin rajista na gwaji, da kuma nuna goyon baya kan hade ci gaba a yankin gwaji na yankin kogin Yangtze mai fadin muraba’in kilomita dubu 358 dake yammacin birnin Shanghai, wanda ya kunshi birane 41 na birnin Shanghai da larduna Jiangsu da Zhejiang da Anhui.
An kafa yankin ciniki maras shinge na Lingang ne a shekarar 2019, shekaru uku da suka gabata, a karkashin jagorancin managartan manufofin kasar, ma’aunin tattalin arzikin yankin yana karuwa da kaso 20 bisa dari a ko wace shekara.
Mataimakin darektan hukumar kula da harkokin yankin Zhao Yihuai yana mai cewa, “Nan gabayankin Lingang zai kara nuna kwazo da himma domin samun sabon ci gaba a wasu muhimman fannoni, ana sa ran babban taron wakilan JKS karo na 20 da za a kira, zai kara kuzari ga yankin yayin da yake kokarin samun ci gaba mai inganci ta hanyar bude kofa ga ketare.”
A filin gina cibiyar nazarin Qingpu ta kamfanin Huawei, manajan kamfani na ukun a rukunin aikin gine-gine na kasar Sin wato CSCEC Yang Wei ya gaya mana cewa,“An kammala mataki na farko na aikin gina cibiyar, lamarin da ya alamta cewa, aikin kamfanin a filin ya shiga wani sabon mataki.
Yayin da babban taron wakilan JKSkaro na 20 ke karatowa, ya dace mu ma’aikatan dake aikin gine-gine mu kara himma domin shirya wa babban taron.”
Tun a farkon bana ne, aka fitar da sabbin manufofin da yawansu ya kai 15 ayankin gwaji na yankin kogin Yangtze, inda ake amfani da kwararru da kudade yadda ya kamata tsakanin lardunan da abin ya shafa.
Mataimakin darektan hukumar zartaswa na yankin Zhang Zhongwei ya yi mana bayani cewa, “Za mu nace kan tsarin kirkire-kirkire yayin gudanar da ayyuka, ta yadda za a ingiza hadin gwiwa da ke tsakanin larduna, mun shiryawa babban taron wakilan JKS karo na 20 ta hanyar daukar hakikanin matakai.”
Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin
Za a kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sinwato CIIE karo na biyar a birnin Shanghai a ranar 5 ga watan Nuwamban dake tafe, rahotannin da aka gabatar sun nuna cewa, adadin manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda za su halarci bikin ya zarta 280.
Mataimakin babban manajan cibiyar taron nune-nune ta birnin Shanghai Wang Xuhong ya bayyana cewa, tun daga watan Yunin bana, ya fara yin aikin share fage tare da abokan aikinsa, yana mai cewa, “Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin da ke karkashin kulawar babban sakatare Xi Jinping ya shaida cewa,manyan baki na gida kasar Sin da na ketare suna gudanar da cinikayya da more kyakkyawar makomarsu tare.”
Dakin taro na Zhangjiang
Dakin taro na Zhangjiang yana cibiyar kimiyya ta Zhangjiang da ke yankin Pudongna birnin Shanghai, inda aka kira babban taron fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI na kasa da kasa a watan Satumban da ya gabata, nan gaba zai kasances abon dandalin kirkire-kirkiren kimiyya a yankin Pudong, da ma birnin Shanghai baki daya, inda ake iya yin cudanya da sabbin fasahohin zamani.
A watan Nuwamban shekarar 2018, babban sakatare Xi Jinping ya taba gaya wa masanan kimiyya da ke aiki a cibiyar kimiyya ta Zhangjiang cewa, “Ya dace a karamai da hankali kan kirkire-kirkiren kimiyya, ta yadda za a samu ci gaba yadda takamata.”
Kawo yanzu gaba daya an kafa kamfanoni kusan dubu 23 a cibiyar, daga cikinsu, kamfanonin fasahohin zamani sun kai sama da 1800.
Mataimakin shugaban yankin Pudong Wu Qiang ya yi tsokaci da cewa, “An kafayankin jagora game da gina tsarin gurguzu na zamani a yankin Pudong, hakki ne da ke wuyan birnin Shanghai, wanda kwamitin kolin JKS ya dora masa, don haka, ya kamata mu kara kokari domin ba da jagoranci ga sauran sassan kasar a wannan bangaren.”
Sabuwar unguwar Fukangli
Sabuwar unguwar Fukangli wadda ake kira unguwar Fukangli a baya, tana yankin Jing’an dake tsakiyar birnin Shanghai, an fara aikin sabunta unguwar ne shekaru 20 da suka gabata, don haka ake kiran ta sabuwar unguwa.
Kwanan baya sakatariyar kungiyar JKS ta unguwar WeiYing ta halarci taron tattaunawa kan yadda za a kyautatatsarin gudanar da harkokin unguwannin birnin, da gina tsari na zamani game da tafiyar da harkokin birnin, tagaya mana cewa, “Muna yin kokari matuka a karkashinjagorancin JKS, domin kyautata sharadin rayuwa na mazauna unguwarmu, muna fatan za a kira babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara, ko shakka babu za mu aiwatar da manufofin JKS masu inganci aunguwarmu ta hanyar kyautata muhallin unguwar, da samar da tallafi ga tsofaffi da sauransu, ta yadda mazauna unguwarmu ta Fukanli za su kara jin dadin rayuwarsu nayau da kullum.”
Alkaluma na baya-bayan nan da aka fitar sun nuna cewa, duk da cewa ana fuskantar tasirin yaduwar annobar cutar COVID-19 a fadin duniya, amma adadin kayayyakin da ake shigowa daga ketare, da adadin kayayyakin da ake fitarwa zuwa ketare, da adadin jarin waje da ake amfani da shi a birnin Shanghai a watanni bakwai na farkon bana wato tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, dukkansu sun karu yadda ya kamata, ana iy acewa, ana samun ci gaba mai inganci a birnin Shanghaina kasar Sin.
(Marubuciya: Jamila daga CMG Hausa)