Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace samar da cikakkun bayanan kididdigar Jama’a, wata dama ce ta samar da ci gaba, sannan kuma duk wat aGwamnati mai kyakkyawan hange samun nasara, ya zama wajibi ta san adadin al’ummar da ke bukatar ababan more rayuwa akowa ne bangare, kamar haske nwutar lantarki, ruwan sha, gidaje, harkar Lafiya da Ilimi.
Kamar yadda Daraktan yada labaran Ofishin Mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge ya Shaida wa LEADERSHIP Hausa.
- Bukatar ‘Yan Siyasa Su San Kalaman Da Za Su Furta Lokacin Kamfen
- 2023: Ana Rububin Kujerar Ahmed Lawan Bayan Soke Takararsa
“Kidaya wani gimshiki ne na gina wa tare da samar da zorewar ci gaba” In ji shi Gwamnan wanda mataimakinsa kuma dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya wakilta, Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki kan shirin Kidayar Shekara ta 2023 da kuma Kidayar Gidaje mai taken “Kidayar Shekara ta 2023- Tabbatar da shigar da Jama’a cikinta” wanda aka gudanar a babban dakin taro na Coronation da ke Fadar Gwamnatin Jihar Kano.
“Dukkanin al’umma wakilai ne kuma wadanda zasu amfana da wannan mataki ne, saboda haka ilimin shirin Kidaya ta Kasata fuskar fadin Kasa, kasafi da fannonin tsumi da tanadi duk ana bukatarsu wajen tsare tsaren gudanar da Kidaya wanda hakan wani tubali ne na aiwatar da harkokin Gwamnati.”
“Mun Gamsu kwarai da samarda kayan aikin irin na zamani wanda Hukumar Kidayar ta samar domin tabbatar gudanar da kidayar ta hanyar zamani a Nijeriya wanda hakan zai tabbatar da samun ingantattun bayanai.
“Ya ci gaba cewa, Gwamnatinmu na bukatar sabbin kunshin bayanai wanda zai tabbatar da aiwatar da sabunta dokokin kidayar domin dorewar ci gaba da sauran tsare tsaren Gwamnati ga kowane bangare na al’umma.
A cewarsa, Jhar Kano muna minta da cewar Hukumar kidayar na da karfi kuma a shirye take wajen tabbatarwa da Kasar nan Ingantacciyar Kidaya wadda kowazai gamsu da ita a Shekara ta 2023.
Gwamnan ya tabbatar da samun goyon bayan Gwamnati tare da Jajircewa domin tabbatar da nasarar gudanar da kidayar domin amfanin al’umma baki daya.
Kwamishinan Hukumar kidayar na Kasa reshen Jihar Kano Dakta Isma’ila Lawal Sulaiman ya bayyana cewa babbar nasarar da ake fatan samu kan kidayar shi ne gudanar da Ingantacciyar kidaya kuma karbabbaya wanda zata sake fasali tare da kai wa ga ingantaccen Matsayi kamar na kasaahen duniya, don haka akwai bukatar shigowar dukkanin masu ruwa da tsaki domin samun kyakkyawan sakamakon bayanai wanda zasu gamsar da matakin da ake bukata.
Cikin wadanda Suka halarci taron akwai ‘yan Majalisar zartarwar Jihar Kano, Sarakunan Gargajiya, kungiyoyin Mata da matasa, abokan mu’amala da kungiyoyi masu zaman kansu.