Dan takarar majalisar dattawa na Kano ta tsakiya karkashin jam’iyyar NNPP, Sanata Ahmad Rufai Sani Hanga ya bayyana cewa yadda jam’iyyar NNPP ta samu karbuwa cikin karamin lokaci a Nijeriya ya nuna alamun nasara a zaben 2023.
dan takarar ya bayana haka a wani taron manema labarai da ya kira a Kano a ranar Talata da ta gabata kan lamarin takararsa da ake managa a halin yanzu.
- NUJ Kebbi Ta Yi Alhini Rasuwar Tsohon dan Jarida Ibrahim Argungu
- Hunkuncin Sauke Wa Mamaci Alkur’ani Bayan Ya Mutu
Sanata Hanga ya ce wannan takara ta kasance wata sa’a ce da Allah Madaukakin Sarki ya ba shi tun da ba nema ya yi ba, domin a can baya an ce ya zo ya yi wannan takara ya ce ba zai yi ba wanda aka bai wa Sanata Ibrahim Shekarau takarar.
Ya ce Shekarau na fita daga NNPP ne jagoran Kwankwasiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a NNPP, ya ce ya zo ya yi, saboda haka shi yana ganin wannan wata sa’a ce da Allah ya ba shi.
Ya ce, “Gyadar dogo Allah ya yi min ba wai tsalake rijiya na yi da baya ba a wannan takara, wato ba rigima muka yi da wani ko wasu ba na karba da kyar Allah ne ya ba ni wannan takara da ke cike da nasara.”