Gwamnan Jihar Gambe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewar cikin shekaru 26 da kirkiro jihar an samu dimbin nasarori na kyautata rayuwar al’umma da bunkasa jihar.
Gwamnan wanda ke jawabi a yayin bikin shekaru 26 da kirkiro Jihar Gombe da kuma shekara 62 da samun ‘yancin kan Nijeriya, ya daura da cewa bikin murna da kafuwar Gombe ya ba su damar yin waiwaye kan abubuwan da aka gabatar da abin da ya kamata su yi a nan gaba don cimma muradun iyaye jagororin da suka tsaya wajen samuwar jihar don ganin jihar ta kasance mai cike da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba, kuma jihar da ake damawa da kowa a cikinta.
- Manchester United Ta Kafa Mummunan Tarihi A Watannin Oktoba
- Yadda Ake Tabbatar Da Ci Gaba Mai Inganci A Birnin Shanghai Na Kasar Sin
Ya ce: “Akwai ababe masu kamanceceniya da juna da dama da suka kai ga samun ‘yancin kan Nijeriya da kirkiro jiharmu
lta Gombe. Baya ga kasancewarsu dukka a ranar daya ga watan Oktoba, kokarin samar da su din duk ya faru ne sakamakon hadin kai da sadaukarwa da jajircewa da kuma fatanmu na kasancewa tsintsiya madaurin ki daya.
“Ina sa ne da nauyin da aka dora min. Na himmatu kuma tare da goyo baya da addu’o’inku, ina jan ragamar wannar jiha ya zuwa turbar ci gaba.
“Ba za a ce rayuwarmu a matsayin jiha bayan kirkiro ta baya tattare da kalubale ba, to amma bisa goyon baya da addu’o’inku, babu wasu kalubalen da ba za mu iya shawo kan su ba. Babu kaidi ga irin nasarorin da za mu iya cimmawa.”