Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce nan ba da dadewa ba kungiyar za ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi.
Osodeke ya bayyana haka ne a wani taro da suka yi da shugabannin majalisar wakilai a ranar Litinin a Abuja.
- Ka’idar Sin Daya Tilo A Duniya Ke Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Mashigin Tekun Taiwan
- Yawan Jama’ar Sin Na Ci Gaba Da Karuwa Kana Yanayin Aikin Yi Bai Sauya Ba
Ya ce daga abin da kungiyar ta gani a wurin taron “akwai alamun nasara. ”
“A wannan karon ana fatan ba za a samu wasu mutane ko kungiya da za su haifar da al’amuran da za su sa kungiyar ta shiga cikin wani mawuyacin hali,” in ji shi.
Ya kuma yi fatan cewa shiga tsakani da shugabannin majalisar za su yi shi ne na karshe saboda dalibai, inda ya kara da cewa fafutukar da ASUU ta yi na neman tsarin ilimi da jami’o’i ne a kasar nan.
“Muna fatan nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za mu kawo karshen wannan yajin aikin.
Osodeke ya ce “Muna son samun tsarin da sake lissafin ya isa ya jawo malamai a duk duniya zuwa jami’o’inmu.”
Ya ce ya kamata kuma a rika biyan jami’o’in Nojeriya da kudi mai tsoka domin jawo hankalin daliban kasashen waje, yayin da ya nuna damuwa kan wasu nagartattun malamai da ke barin kasar.
“Mu ne manyan Afirka kuma dole ne mu rayu tare da wannan.
Ya ci gaba da cewa, “Muna godiya ga shugaban majalisar kan wannan shiga tsakani kuma dole ne mu hada kai domin kowane dan Nijeriya ya yi alfahari da jami’o’in da muke da su.”
Ya ce bai kamata yajin aikin ya wuce makonni biyu ba, “da majalisar dokokin kasar ta sa baki kafin yanzu”.
Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce tsoma bakin da shugabannin majalisar suka yi ya yi tasiri.
Gbajabiamila ya kuma ce ganawar da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nisa.
Ya ce za a sanar da mataki da aka yanke ga kungiyar da jama’a a ranar 11 ga Oktoba.
Ya ce shugabannin majalisar sun samu damar tabbatar da cewa an samar da dukkan bukatun ASUU na farfado da albashi da sauransu a kasafin kudin 2023.
Ya ce an saka Naira biliyan 470 a cikin kasafin kudin 2023 don biyan bukatar ASUU.
“An warware matsalar UTA kamar yadda gwamnati da ASUU suka amince kuma dukkansu za su zauna su amince da sanya duk wasu abubuwan da ASUU ke bukata a tsarin biyan kudin IPPIS.
“Na yi imani mun rufe kasa, kuma shi ne ainihin abin da muka amince da shi.
“Muna ASUU ta janye yajin aikin yau da fatan nan da kwanaki biyu masu zuwa.
“Muna gode wa ASUU saboda amsa kira a duk lokacin da muka kira su.
“Mun hadu a ofishina don tattaunawa. Mun yi haka ne don kare bukatar dalibanmu,” in ji shi.