Hukumar Kwastam karkashin sashen ayyukan tarayya, na shiyyar “D” da ke Jihar Bauchi, ta kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai sama da Naira miliyan 200 da aka daga watan Agusta zuwa yanzu.
Kakakin hukumar na NCS, FOU, Bauchi, Umar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu, kuma aka raba wa manema labarai a jihar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa, rundunar tarayya ta kunshi jihohin Bauchi, Yobe, Adamawa, Taraba, Borno, Plateau.
- Yawan Jama’ar Sin Na Ci Gaba Da Karuwa Kana Yanayin Aikin Yi Bai Sauya Ba
- Wata Sabuwa: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fasinjan Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna A Hanyarsa Ta Komawa Garinsu Bayan Kubutarsa
Jihohin Benuwe, Gombe, da Nasarawa; mai hedikwata a Bauchi. Ya ce daga cikin kayayyakin da aka kama sun hada da: buhu 542 na buhunan shinkafa na kasar waje mai nauyin kilo 50, buhu hudu dauke da harsashi kilo 165 na pangolin, buhuna 487 na takin Urea da kuma katan 250 na taliyar kasar waje.
Sauran sun hada da bales 191 gwanjo, galan 110 na man fetur, katan 70 na sabulun waje da lita 25 na kanazir.
Abdullahi ya ce akalla motoci bakwai daban-daban da ake amfani da su wajen kai kayayyakin da aka hana jami’an hukumar suka kama su.