An kashe kasurgumin jagoran ‘yan ta’adda Ali Dogo tare da mayakansa da dama a Jihar Kaduna.
An kashe wadanda ake kira Yellow, Dogo da ’yan ta’adda a wani samame ta sama da rundunar Operation Whirl Punch ta kai.
- Masanin Birtaniya: Duniya Ta Amince Da Ci Gaban Da Sin Ta Samu A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
- NUJ Kebbi Ta Yi Alhini Rasuwar Tsohon dan Jarida Ibrahim Argungu
Wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaida cewa tun da farko shugaban da yaransa sun tsere daga Jihar Neja.
Sun koma gidan wani Alhaji Gwarzo da ke Yadi a karamar hukumar Giwa.
Sojoji sun samu wannan bayanin inda suka aike da rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) wadanda suka kone ginin da suke ciki.
Wani farmakin da aka kai ta sama ya kai mai nisan kilomita 33 a arewa maso yammacin Mando a Kaduna.
Shugabannin ‘yan ta’adda da sauran yaransa an yi musu luguden wuta tare da shafe mahara da dama.
Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya ce za a ci gaba da kai farmakin tare da hadin gwiwar sojojin kasa.
An kaddamar da Op Whirl Punch wani rukunin Op Sharan Daji ne da ke kula da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, kewayen Birnin Gwari da Jihar Neja.