Ministan Sadarwa na Najeriya, Farfesa Isa Fantami, ya shaida cewa Ma’aikatar sa ta kammala ayuyyuka sama da 2000 a cikin shekaru 3 (uku) don inganta harkokin sadarwa a duk fadin kasar nan.
Yayi wannan furucin ne na lokacin wata ziyara bude ido da ya kai a cibiyar sadarwa (Data) ta kasa (Galaxy Backbone Ltd. Abuja) ranar Alhamis din makon jiya, inda yace cibiyar baya ga amfanar da ma’aikatacin gwamnati, har ma da masu zaman kansu hade da duk yan Najeriya.
A cewar shi, ” wannan Cibiya ta Gwamnatin Tarayya idan a kammala, zai kasance muhimmin ma’aikata ne ta kasa wanda ina fata na ba da da arewa ba, za’a kammala kuma ina tabbatarwa “yan Najeriya cewa Cibiyar zata bunkasa ilmin sadarwar zamani a Najeriya”.
Fantami ya kara da cewa, Santar wuri ne na horaol da yan Najeriya kuma zai bada ayuyyuka ko da ga Gwamnati ko masana’antu masu zaman kansu koma ma’aikatoci ko kungiyoyi daga kasashen ketare, don haka sai yayi kiran ga’yan Najeriya da su rungumi wannan damar ba tare da sun dogara da Gwamnati ba, ko kuma aiki a cikin gida kowai amma su kai ga nema har kasashen waje.
Ministan ya kara da cewa, akwai ayuyyuka dubbai a wadamnan kasashen ketare, saboda haka, abu da ake bukata kawai shine mutum yana da ilmin akan abin da yake sha’awa yin kuma a shirye yake ya rungumi duk wata kalubale.
” Don haka, idan yan kasa sun samu baita da horo a wadannan fannomi, dams ce a gare su wajen samun ayuyyukan yi baa cikin Najeriya kawai ba, har ma da kasashen ketare da kuma gwarajen ma’aikatun kimi ya ma,” yana mai karawa da cewa, Cibiyar Data ta Kano tuni ta soma aiki, kuma na bada dadewa ba, za’a kaddamar da ita.
A nashi jawabin, Babban Darekta na Galaxy Backbone, Farfesa Muhammed Abubakar, ya aiyana cewa, Santocin Data jagora ce ta sadarwar za mani (ICT) a duk fadin duniya, kuma suna da duk hanyoyi da kimiyar Santa ta Data inda mutum zai samu duk bayanan da yake bukata.
Ya kara da cewa, a baya, “muna tattara bayanan Sirrin mu ne a cikin kundi (files), kuman falilan me suke da damar yin bincike a cikin su. Amma a yau, Datar sadarna ta kai ga ko ina, kuma duk bayanan da kake bukata a kasa, suna nan a cikin Santa – Santa ta cibiyar Data a dunkule a hannun ka”.
Ya ce idan mutum yana da Datar da bata da kariya, to komai zai iya faruwa”. Ita dai Galaxy Backbone Ltd (GBB), Cibiyar sadarwa ce ta Najeriya don amfanin ma’aikatun Gwamnati da masu zaman kansu, da take karkashin Ma’aikatar Sadarwa ta Najeriya mai alhakin lura da bayanai a cibiyoyin Data a fadin kasa.