Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin kafofin watsa labarai na gwamnatin tarayya da masu zaman kansu a jihar bisa dauko wa da yada rahoton gangamin jam’iyyar adawa ta PDP.
An kuma umarci kwamishinan ‘yansanda na jihar da ya cafke dukkanin ‘yan jaridar da suka halarci wajen gangamin domin dauko labarin.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Aure ‘Ya’yan Tsohon Akanta-Janar Na Zamfara Da Suka Sace
- Da Sa Hannun Gwamnatin Zamfara ‘Yan Daba Suka Farmake Mu – Dan Takarar Gwamna A PDP
Wannan umarnin ya fito ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Malam Ibrahim Magaji Dosara, da ya yada a kafafen yada labarai na jihar.
Kafafen da umarnin rufewar ta shafa sun hada da, gidan rediyon tarayya (Mallakin gwamnatin tarayya), gidan talabijin na kasa NTA, gidan rediyo masu zaman kansu na Pride FM da Gamji hadi da wasu da aka samu da dauko rahoton.
A cewar kwamishinan an kulle gidajen yada labaran ne kan saba umarnin da majalisar tsaro ta jihar ta bayar na dakatar da dukkanin harkokin siyasa a jihar sakamakon yawaitar ayyukan ‘yan ta’adda a wasu sassan jihar.